Rigimar APC:Jagororin Jam'iyya Na Jiran Matsayar Buhari Bayan Zama Da Wasu Makusantansa A Landan

Rigimar APC:Jagororin Jam'iyya Na Jiran Matsayar Buhari Bayan Zama Da Wasu Makusantansa A Landan

Manyan jagororin jam'iyya da gwamnoni da mambobin kwamitin rikon kwarya na APC sun matsu suna jiran matsayar da shugaban kasa ya cimma a zaman tattaunawa da ya yi da wasu makusantansa a birnin Landan kan rikicin da ya dabaibayi APC.

Bayan Ministan Shari'a Abubakar Malami da Ministan Ilmi Malam Adamu Adamu da Ministan harkokin jirgin sama Sanata Hadi Sirika da Faruku Adamu Aliyu, rahotanni na nuna akwai wasu jiga-jigan gwamnatin Buhari dake a Landon din.

Shugaban rikon kwarya na APC Mai Mala Buni yana a London shi ma  ya bar Dubai in da ya je duba lafiyarsa a ranar Alhamis a satin da ya gabata.

Ana sa ran Buhari zai kawo karshen tirka-tirkar ya fadi kai tsaye abin da yake son a aiwatar a jam'iyar ta APC.

Wata majiyar ta bayyana cewa Buni zai shiga ofis na shugabancin APC a ranar Litinin bayan ya dawo Nijeriya.

"Yanda ake yanzu a APC shugaba Buhari ne zai warware komai a tsakanin gefen Buni da wadanda ke goyon bayan gwamnan Neja Abubakar Sani Bello, ana dakon matsayar da aka cimma a zaman da aka yi a Landan.

"Kowane irin umarni ne Buhari ya bayar dukkan shugabanni da gwamnoni da mambobin kwamitin rikon kwarya za su yi biyayya kansa, a kowane bangare akwai fargaba domin matsayar Buhari ce za ta nuna yanda jam'iyar za ta tafi"a cewar majiyar.