#DAMUWA: Yadda Za'a Gane Ciwon Damuwa Ya Kama Mai Shanyewar Ɓarin Jiki
Damuwa larura ce mai zaman kanta kamar sauran larurori da ke kai mutum ga ganin likita.
Bincike da dama sun nuna cewa kaso ɗaya cikin uku na majinyatan shanyewar ɓarin jiki suna fama da damuwa musamman a shekarar farko.
Damuwa larura ce da ke shafar lafiyar ƙwaƙwalwa, tunani, hankali da walwala.
Majinyatan shanyewar ɓarin jiki suna gamuwa da larurar damuwa sakamakon nakasa, kassarewa ko asarori da suka gamu da su biyo bayan shanyewar ɓarin jikin.
Bayyanar wasu baƙin ɗabi'u saɓanin sanannun halayen mutum kafin shanyewar ɓarin jiki shi ke nuni da cewa damuwa ta kama majinyancin shanyewar ɓarin jiki.
Alamomin sun haɗa da:
1. Bacin rai ko fushi.
2. Saurin fusata ko tunzira musamman kan ƙanƙanin abu ko kuma haka-kawai.
3. Raina kai, ɗeɓe ƙauna ko haso, fidda rai ko jin gaza taɓukawa.
4. Gushewar sha'awar ababen so kamar wasu abubuwa da mutum ke son su kafin shanyewar barin jiki kamar son karance-karance ko wani abinci ko kuma wasu ayyuka kamar wasanni da sauransu.
5. Rashin kuzari ko matsananciyar kasala.
6. Rashin mai da kai yayin da ake tattaunawa kan wani abu, wahalar tunawa da lamuran da suka shuɗe, wahalar zaɓi ko yanke hukuncin nan take.
6. Matsalolin bacci: Gaza samun bacci, farkawa da wuri ko yawan baccin.
7. Gushewar sha'awar cin abinci.
8. Zaɓar mutuwa ko barazanar kashe kai, da dai sauransu.
Haka nan, duk da cewa abu ne mai wahala a iya gane takamaiman sababin damuwa ga mai shanyewar ɓarin jiki, amma ana alaƙanta sababin damuwar da wasu matsaloli daga iyali, dangi ko al'umma kamar haka:
1. Rashin kyakykyawar kulawa, yin watsi ko buris da majinyaci.
2. Ƙauracewar iyali, dangi, abokai ko abokan hulɗa.
3. Rashin tallafi musamman domin kula kai da kuma ɗawainiyar asibiti.
4. Mai da majinyaci komabaya musamman yayin tattaunawa, shawarwari ko yanke hukunci.
Abin takaici ne kwarai, a ce yayin da mutum ke fama da shanyewar ɓarin jiki sannan kuma a ce larurar damuwa ta sake samun sa.
Har wa yau, kasancewar aikin likitocin fisiyo na dawo da aikin ɓarin da ya shanye yana da jiɓi da koyo da kuma bayar da umarnin aiki, damuwa na kawo cikas ƙwarai da gaske ga warakarsu. Hakan yana ƙara wa likitan fisiyo wahalar ganinsu sannan yana kawo tsawaitar lokacin warkewa.
Da zarar an lura da waɗannan alamomi na damuwa, a tuntuɓi likita.
managarciya