Bayan Shekara 2, Ɗaliban FGC Yauri 4 Sun Shaki Iskar Yanci

Bayan Shekara 2, Ɗaliban FGC Yauri 4 Sun Shaki Iskar Yanci

Ɗaliban makarantar kwalejin gwamnatin tarayya (FGC) da ke birnin Yauri a jihar Kebbi huɗu daga cikin 11 da suka rage hannun yan bindiga, sun shaki iskar yanci. 

Jaridar Daily Trust ta ce ɗaliban mata huɗu sun kubuta ne shekara biyu bayan yan bindigan sun yi awon gaba da su daga makaranta a jihar Kebbi.

Ɗaliban guda huɗu, Bilha Musa, Faiza Ahmed, Rahma Abdullahi da kuma Hafsa Murtala, sun kubuta daga hannun ƙasurgumin ɗan bindiga, Dogo Gide, ranar Jummu'a da yamma.
"Sai da aka kwashe kwanaki 6 ana tattaunawa a cikin Daji kafin a samu nasarar kubutar da ɗaliban mata guda huɗu." 
"Har yanzu muna da ragowar ɗalibai Bakwai da suke tsare hannunsu kuma iyayen biyu daga cikinsu na can cikin jejin suna kokarin kubutar da su." 
Kaoje ya kara da cewa sai da iyayen suka biya kuɗin fansa wanda ba'a san adadin yawansu ba gabanin kubutar da yaran. Sun sayar da kadarorinsu kuma wasu yan Najeriya sun tallafa musu. 
A watan Janairu, Salim Kaoje, ya tabbatar da cewa sun fara tattaunawa da Dogo Gide bayan sun nemi mahaifiyarsa ta shige musu gaba, kamar yadda Ripples ta rahoto. 
A ranar 17 ga watan Yuni, 2021, 'yan bindiga suka farmaki FGC Birnin Yauri, inda suka yi awon gaba da gwamman ɗalibai da malamai a makarantar mai ƙunshe da maza da mata.