EFCC Ta Gurfanar Da Tsohon Shugaban   Jami'ar Tarayya Dake Gusau Kan Almundahana

Hukumar na zargin mataimakin shugaban Jami'ar da karbar kudade daga hannun 'yan kwangila da kuma yin takardun jabu domin samun kudade daga hannunsu. 

Hukumar yaki da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta gurfanar da shugaban Jami'ar Gwamnatin tarayya dake Gusau Farfesa Magaji Mukhtar gaban wata babbar kotun tarayya dake Jabi a babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata kan zargin badakalar kudade.
Hukumar na zargin mataimakin shugaban Jami'ar da karbar kudade daga hannun 'yan kwangila da kuma yin takardun jabu domin samun kudade daga hannunsu. 
Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC tana hoƙoron yaƙi da cin hanci a ƙasar Nijeriya.