Ban Da Burin Zama Shugaban Ƙasa A 2023-------Nasir El-Rufa'i

Ban Da Burin Zama Shugaban Ƙasa A 2023-------Nasir El-Rufa'i

Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i ya ce baya da wani burin zama shugaban ƙasa a 2023, ya yi alƙawalin mara baya ga duk ɗan takarar shugaban ƙasa da ya fito daga kudancin Nijeriya.
Gwamnan ya sanar da hakan ne a lokacin da yake karɓa tambayoyi a fadar shugaban ƙasa dake Abuja.
Nasir ya yi fatan duk wanda zai gaje shi  daga cikin mutanensu ne, mutanen Kaduna ne za su zaɓi wanda suke so shi ba zai ce ga wanda yake so ba.
Ya ce yafi damuwa kan wanda zai zama gwamnan Kaduna fiye da wanda zai zama shugaban ƙasar Nijeriya.
Ya ce yana da kulawa kan wanda zai gaje shi, amma baya da wani buri na gaba kan mulki "ina son na kammala wannan aikin na koma gudanar da rayuwa ta da ta shafe ni, na sake rubuta littafi na ƙara samun kuɗi masu yawa."