Ana Cikin Tsadar Rayuwa Gwamnan Wata Jiha   Zai Ɗauki Sabbin Malamai 5,000 

Ana Cikin Tsadar Rayuwa Gwamnan Wata Jiha   Zai Ɗauki Sabbin Malamai 5,000 

Gwamnatin jihar Osun ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ademola Adeleke ta amince da daukar sabbin malamai 5,000 da ma'aikatan ilimi 250.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, gwamnatin za ta ɗauki malamai da sabbin ma'aikatan ne domin cike gibin da ke akwai a harkokin koyarwa na jihar. 
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da gwamnatin ta fitar mai ɗauke da sa hannun sakataren watsa labaran gwamna, Olawale Rasheed, ranar Laraba a Osogbo. 
A sanarwan, Gwamna Adeleke ya ce ya amince da ɗaukar sabbin malaman ne bayan kammala nazari da tantance buƙatun da ke akwai wanda gwamnatinsa ta yi a 2023. 
Mista Rasheed ya kara da bayanin cewa an cimma wannan matsaya ne a wurin taron majalisar zartarwa ta jihar (SEC) bisa jagorancin Gwamna Adeleke. Bugu da ƙari, ya ce majalisar ta umarci ma'aikatar ilimi ta gaggauta bin duk matakan da ya dace na ɗaukar aiki domin zaƙulo kwararru kuma masu gogewa. 
A cewarsa, samun kwararrun malamai zai inganta harkar koyo da koyarwa a jihar da ke Kudu maso Yammacin Najeriya, rahoton Tribune Online.