Dakarun Sojojin Sama Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Masu Tarin Yawa a Arewacin Najeriya 

Dakarun Sojojin Sama Sun Hallaka 'Yan Ta'adda Masu Tarin Yawa a Arewacin Najeriya 

Rundunar sojojin saman Najeriya ta bayyana cewa jiragenta sun kai farmaki kan maɓoyar ƴan ta'adda a jihohin Kaduna da Zamfara. Rundunar sojojin ta bayyana cewa a yayin farmakin, dakarunta sun hallaka ƴan ta'adda masu tarin yawa. 

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, AVM Edward Gabkwet, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton jaridar The Nation. 
AVM Edward ya bayyana cewa an kai hare-haren ne a ranar 21 ga watan Agustan 2024 a dajin Mallum da ke jihar Kaduna, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar. Kakakin ya bayyana cewa bayanan sirri sun nuna cewa ƴan ta'addan waɗanda suka samu mafaka a jihar Kaduna su ne ke da alhaki kan hare-haren da ake kai wa kan fararen hula a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja. Ya ƙara da cewa an hango ƴan ta'addan bayan sun gama ta'addancin su a dajin Alawa na jihar Neja suna tahowa zuwa maɓoyarsu a dajin Malum cikin ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna. 
"Nan da nan dakarun sojojin sama suka yi shiri tare da kai hare-hare ta sama a ranar, 21 ga watan Agustan 2024 kan maɓoyar ƴan ta'addan da ke dajin Malum." "Ɓarnar da aka yi musu a harin da kuma bayanan da aka samu daga majiyoyi a yankin, sun nuna cewa an hallaka ƴan ta'adda masu yawa a yayin harin." "Haka kuma an kai irin waɗannan hare-haren a maɓoyar ƴan ta'adda da ke Bayan Ruwa a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara." - AVM Edward Gabkwet.