'Yan bindiga sun kashe mutane da yawa a Sokoto lokacin da suka kai hari a Sansanin Sojoji
'Yan bindiga sun kai harin kwanton ɓauna a Sansanin sojoji dake cikin ƙauyen Dama ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.
'Yan bindiga sun kai harin kwanton ɓauna a Sansanin sojoji dake cikin ƙauyen Dama ƙaramar hukumar Sabon Birni a jihar Sakkwato.
Majiyar ta shaidawa daily trust cewa harin ya faru ne a ranar Jumu'a data wuce.
Tsohon Shugaban ƙaramar hukumar Idris Muhammad Danshadi ya tabbatar harin kuma ya ce da yawan sojoji sun ɓace a farmakin.
Maharan sun ƙone motocin aiki biyu na sojoji sun tafi da wata da suka zuba abincin da suka sace a ƙauyen.
Ya ce sun samu bayanin hari biyu da aka kawowa mutanen wurin don suna amfani da layin sadarwa na ƙasar Nijar.
Haka ma wani basarake a yankin ya tabbatar da cewa an tura motoci a kwashe gawar sojojin. Sama da mota 10 ta sojoji sun shiga cikin daji don farautar maharan.
Wani jami'in tsaron Sibil defens ya ce abokan aikinsa uku ne ke cikin waɗanda aka kashe.
Haka Maharan sun shiga ƙauyen Katsira sun harbe mutum hudu mutum biyu daga cikinsu na karɓar magani biyu daga cikin sun rasu nan take
Maharan sun yi garkuwa da wasu mutane a ƙauyen sun tafi da su a cikin dajin.
managarciya