ƘADDARA TA: Fita Ta Takwas

ƘADDARA TA: Fita Ta Takwas

ƘADDARA TA: 


        Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 8*


                  ~Sunyi kwana biyar a asibiti kafin aka sallamesu, da kyar yake takawa sabida ciwon da yake cikinshi, wajen jeep ɗin dake fake suka nufa tareda ya kaseem da yayi kyau cikin yadi maroon, Aneeta kuma sunye take da hijab peach color tayi kyau sosai tasa mayafin a kanta bayan tasa hula me kyau baƙi, tana rike dashi yana takawa a hankali har ya shiga motan, itama shiga tayi sannan ya kaseem ya shiga, driver ne yaja suka tafi, koda suka isa gida a hankali yake tafiyan har aka kaishi ɗaki, kwanciya yayi akan gadon yayi shiru yana kallon Aneeta dake kallonshi, gira ya ɗaga mata alaman ya akayi?
murmushi tayi ta kauda kai, zata tafi yaja hanunta ta faɗo kanshi, rungumeta yayi sosai yana sauke ajiyan zuciya, shiru tayi a jikinshi har zuwa lokacin daya fara shafa duk jikinta, duk wani taɓata da yayi ji take kamar wuta ne yake taɓa mata jiki, bakinshi zai haɗa da nata tayi saurin tashi ta bar wajen, binta yayi da kallo, sultan ne ya shigo yace "yaya yarima a kawo maka abinci?"
gyaɗa kai yayi, yace "to"
fita yayi jim kaɗan yazo da abinci yace "tashi na baka"
tashi yayi ya zauna, jallof rice ɗin ya fara bashi yana ci cikin nutsuwa, fitowa tayi daga toilet ta karɓi plate ɗin tace "karka damu zan bashi"
kallonta yayi shifa gabanshi yana faɗuwa idan yana kallonta ya rasa dalili, tace "tashi mana sultan zan bashi da kaina"
a hankali ya tashi ba dan yaso ba, bashi ta fara, sultan ya fita daga ɗakin, fadeel yaga yanayin sanyin jikinshi yace "ya akayi sultan?"
yayi tsaki kaɗan yace "wallahi haka kawai hankalina yaki kwanciya da Anti Aneeta musamman idan tana tare da ya hameed sai naji gabana yana faɗuwa"
caraf a kunnen Ammi wacce ta fito daga ɗaki, kallon sultan tayi, ashe ba ita kaɗai bace takejin haka akan aneetan shima yana ji, idan taga aneeta gabanta yana faɗuwa, idan tana tare da hameed sai taji bugun zuciyarta yana karuwa, tana kallonsu har fadeel ya dafa wuyanshi suka tafi yana cewa "ka kwantar da hankalinka babu wani abu mara kyau da zatayi mishi kasan tana masifan sonshi"
fitowa Aneeta tayi da plate ɗin a hanunta ido huɗu sukayi da Ammi, murmushi tayi mata tace "sannu ammi"
bata amsa mata ba kuma bata daina kallonta ba, taɓe baki tayi ta wuce taje ta aje plate ɗin ta dawo ta shiga ɗakin ta rufe.
meenat wacce taga duk abinda ya faru tazo wajen ammi ta riketa, tace "ammi me yake faruwa ne?"
girgiza kai tayi tace "ba komai meenat"
tace "ammi amma kamar naga kina yiwa anty Aneeta wani irin kallo kuma naga ya sultan ma kamar jikinshi a mace da ita"
ammi taja numfashi sannan tace "meenat wallahi na kasa nutsuwa da wannan yarinyar haka kawai banason ganinta kusa da hameed"
tace "comon ammi babu komai fa kawai dai kinsa abu ne a ranki"
tace "to amma meenat"
tace "amma me ammi muje please ki huta kin gaji sosai"
shiru tayi suka tafi, meenat kallon kofan ɗakin tayi itama haka kawai taji kamar akwai abu a kasa, itama ta kasa nutsuwa da aneeta tunda Amrah ta mutu, sannan tunda akayi aurensu da hameed sai taga kamar ta canja duk da tana ɓoyewa amma ta lura da hakan.
sharewa kawai tayi.

zaune suke a dinning daka anan ne suke haɗuwa su duka harda Abi, abinci sukeci da hameed wanda yake cin abincin a hankali yake kallon matarshi, murmushi yake idan sun haɗa ido, meenat tace "Abi zanso naje nima naga wani kasan saudiya kawai na taɓa zuwa gaskiya zanso naje wata kasar kuma"
murmushi yayi yace "shikenan meenat zaɓi kasar da kikeson zuwa hutunki"
tace "turkey"
aneeta ta sauke cup na tea da take sha tace "me zakiyi a turkey? akwai sanyi sosai acan gara kije cairo yafi daɗi sabida babu sanyi sosai kuma babu za..."
saurin yin shiru tayi ganin yadda duk suke kallonta bata sani ba ashe tayi ɓarin zanje, meenat da mamaki take kallonta sai kuma tace "ya akayi kika sani? keda kikace baki taɓa fita ko wani gari ba bale wata ƙasa?"
gabanta ya fara faɗuwa da sauri ta kalli ammi wacce ta aje spoon tana kallonta tana jiran amsa, tace "a tv na gani ai, film na kalla ranan naga an faɗa"
sultan yace "wani film?"
ruɗewa tayi domin ta rasa amsan da zata bayar, tace "to ai ba zan iya rike sunan film ɗin ba sabida da turanci ne kuma bana jin turanci"
meenat tace "kuma kikaji me suke cewa a film ɗin har kikaji sunce kasar turkey da sanyi?"
tace "to ai naga suna saka rigan sanyi su kuma..."
kaseem ne yace "ya isa haka"
shiru tayi meenat kuma ta fara binta da kallo haka Ammi, hameed yana gamawa ya tashi ya tafi ɗaki.
itama Aneeta bata jira yau ta gama duka ba ta tashi ta tafi, da kallo meenat ta bita.

tun daga ranan bata kara yadda tayi suɓul da baka ba, yau weekend ne suna zaune a falo su duka banda hameed dake bacci a ɗaki, meenat ce kwance akan sofa tana chatting, tace "yanzu zasusa favorite film ɗina bara na kashe data nayi kallo"
sunan jarumai aka fara nunata tana rike da wayan taji Aneeta tace "michael marrone, ashe kina kallon film ɗinshi wannan film ɗin After marriage ne ko?"
kallon da meenat take mata yasa tayi saurin rufe baki, meenat zuwa yanzu ta gane karya take yi akan abubuwa da dama domin yadda take kiran sunan abu kamar tanada masaniya sosai a kai, shakku ta fara a kanta, batayi magana ba kawai ta kawar da kai tana kallon tv, a zahiri kallo take amma a zuciyarta tana kara kallon Aneeta ne, a hankali tace "ya zama dole nasa ido sosai a kanta"
saida aka gama film ɗin ta musu saida safe ta tafi ɗaki, ta rufe kofan ta jingina da jikin kofan tayi shiru, a hankali ta lumshe ido ta buɗe tace "wacece wannan?"
zata wuce ciki taga sim a gefen gado, da sauri tace "sim ɗin waye?"
ɗauka tayi tana kallo, sai kuma tace "ba nawa bane, ko dai na Amnah ne?"
shiru tayi tana tunani sai kuma tace "no Amnah batada sim biyu saide Amrah itace take canja sim"
da sauri tace "wannan na Amrah ne"
da sauri ta buɗe wayarta tasa sim ɗin a ciki, dubawa ta fara taga sunayen duk yawanci a bakin Amrah takejin sunan, numbern Amnah taga tayi saving da blood sis, tace "tabbas wannan sim ɗin Amrah ne"
barin sim ɗin tayi a wayarta ta kwanta ta fara bacci.
Aneeta kwance take itada hameed ya rungumeta sosai yana bacci cikin kwanciyan hankali, so take ta samu waje tayi waya amma tana tsoron kada a kamata, a hankali ta cire hanunshi daga jikinta kunna wuta tayi taga karfe biyu na dare cikin sanɗa ta buɗe drower ta ɗau waya karami data ɓoye fita tayi daga ɗakin cikin sanɗa take tafiya, tsayawa tayi a jikin bango ta fara kunna wayan saida ya kunnu zata kira taji karan tafiyan mutum, da sauri ta rufe baki tana waro ido, sanye yake da bakin kaya ya rufe fuska kofan jabeer taga ya buɗe, fasa kiran wayan tayi a hankali ta fara bin bayanshi, tsayawa tayi a baya taga ya ɗaga hulan, alluran da ake yiwa hameed kullum taga ya ɗauka ya juyo dashi, zaro manyan idanunta tayi ganin sultan ne ya canja alluran ya ɗau original ɗin ya kalli kaseem dake bacci cikin kwanciyan hankali sannan ya juya zai tafi, da sauri ta ɓuya a bayan kofa, fita yayi ya rufe kofan, yana fita itama ta fita cikin sanɗa tana mugun mamakin me zaisa sultan ya canja allura?
kiran wayan da batayi ba kenan ta koma ɗaki taga hameed ya buɗe ido yana kallonta, tasan da tambaya sosai a ranshi amma ba zai iya furtawa ba, a hankali ta kwanta ta rungumeshi tace "na fita shan ruwa ne kasan na saba da shan ruwan dare"
shafa kanta yayi sannan ya mata kiss a forehead ya kara rungumeta ya lumshe ido, a ranta har yanzu ta kasa gane me yasa sultan zaiyi haka?
tana ganinshi ta cikin dim light yana bacci like innocent baby boy, yadda yake turo baki kamar karamin yaro da ake shayarwa, shafa kanshi tayi a hankali ta fara shafa sajenshi, da sauri ta ɗauke hanunta daga jikinshi ta rufe ido tana cewa "bai kamata ba, bai kamata ba sam Aneeta"
matsawa tayi daga jikinshi tace "ba wannan ya kawoki ba aneeta abinda ya kawoki daban kada kiyi kuskuren da ba zaki yafewa kanki ba aneeta"
pillow ta ɗauka ta rungume, zuciyanta yana tafasa tana jin zafi a ranta.

washe gari breakfast sukeyi Aneeta tayi kyau cikin baƙin kaya, akan ferfesun da take sha idonta yake bata yadda ta kalli kowa ba domin bata bacci idonta kamar na ƴar kwaya ya zama tsaban baccin da takeji, kaseem yana sanye da uniform cikin sauri yake cin abincin saida ya ɗan koshi yace "thank god, tashi hameed nayi maka alluranka sauri nake"
ya ɓata rai sabida baison kalman allura, yace "oya tashi"
badan yaso ba yaga yaja ruwan alluran, idanunta masu cike da bacci ta kalli sultan, baiko kalli inda suke alluran ba, zai mishi tace "ka tabbata alluran bs fake bane?"
jikin sultan ne ya fara rawa, tana kallon cikin idon sultan tace "ina nufin ka tabbata ba'a canja ba?"
cokalin hanun sultan ne ya faɗi, abincin yabi kanshi take ya fara tari, Ammi da meenat sai kallonta suke yadda take jujjuya cokalin tana magana da kwarewa cikin rashin tsoro, kaseem murmushi yayi yace "nifa babban dr ne aneeta sabida mijinki ya samu lafiya kikeso a samu allura me kyau ko?"
murmushin gefen baki tayi har yanzu idonta akan sultan tace "so nake ya samu lafiya ya kaseem amma ka kara duba alluran kada watarana a canja"
gama mishi yayi yace "good boy yanzu ba gashi an gama ba?"
kwanciya yayi a wajen kan sofa, shifa idan anyi mishi alluran maimakon yaji sauki sai yaji jikinshi yana zafi kuma bacci me nauyi mara daɗi saiya ɗaukeshi, bayan ya tashi sai yaji jikinshi yana ciwo kullum haka yake fama, amma ya kaseem ya nace da alluran kuma baison ɓacin ranshi shiyasa yake yadda.

tashi tayi daga wajen ta wuce ɗaki ba tareda ta gama ci ba, ido ta rufe tace "no ba zan bari wani ya kashe hameed ba nice ya kamata na kashe shi da hannuna"
tayi maganan tana kallon dogayen hannayenta.
meenat school ta tafi, bayan ta dawo ta gama aikinta sannan ta zauna a falon tareda su Aneeta kamar kullum suna hira
kiran wayan meenat akayi ta duba taga sim ɗin Amrah da tasa ake kira da sabon number, ajewa tayi bata amsa ba, aka kara kira ta amsa tace "hello"
muryan mace taji tace "Amrah inata kiranki ba zaki ɗauka ba? yau na dawo nigeria naga tun ranan baki kara hawa online ba, ina fatan yanzu kin gane wacece ita, na faɗa miki Aneeta babu wanda bai santa ba a gidanmu"
da sauri ta tashi ta wuce ɗakinta, tace "ki nutsu baiwar Allah wannan ba Amrah bace Amrah ta mutu amma wannan ƴar uwarta ce meenat"
tana jin yarinyar ta kwala ihu tace "ta mutu? ko kuma ta kasheta ko?"
meenat cikin ruɗewa tace "wacece?"
tace "Aneeta lawan lamba"
dafa kirji meenat tayi ta zaro idanu a razane tace "Aneeta lawan lamba?"
tace "tabbas nasan itace ta kasheta"
faɗa mata duk yadda sukayi tayi sannan tana kuka tace "ashe mutuwa tayi"
meenat cikin tashin hankali tace "dan Allah ki faɗamin inda zamu haɗu yau da dare inason ki faɗamin komai"
tace "kece ƴar sarki da take bani labari kullum?"
tace "nice"
tace "shikenan zanzo da dare amma kisan yadda zaki fita kada ki nuna mata kin gano komai kawai ki sameni a bakin titin kwaltan farko zan jiraki"
tace "kamar karfe nawa?"
tace "karfe goma sha biyu sabida banso kowa ya sani"
tace "to na gode me sunanki?"
tace "sunana fauza"
"na gode fauza"
kashe wayan tayi ta zauna a bakin gado tana maimaita kalman Innalillahi wa inna ilaihiraji'un, da kyar ta saisaita kanta ta fito, Aneeta ta kalla sai kuma ta mata murmushi tace "Anty Aneeta ki gyaramin gashina"
tace "zauna"
a tsorace ta zauna amma bata nuna mata ba, har dare tana bin komai a hankali sannan bata nunawa kowa komai ba, kallon agogo take bacci yaki ɗaukanta har karfe sha biyu kafin tasa dogon hijabi ta fita cikin sanɗa, cikin sanɗa ta fita a gidan tana sauri har taje bakin titin, gani tayi babu ita, kiran wayanta tayi taji a kashe, hankalinta ne ya kara tashi tace "fauza kizo mana ina kike?"
jiranta tayi babu ita babu dalilinta, saida ta gaji ga dare ya gama yin nisa kafin ta koma gida jikinta a mugun mace, ɗakinta ta shiga ta zauna kawai tana addu'a a fili da haka har gari ya waye batayi bacci ba, tana zaune akan sallaya tana addu'a, saida ta gama ta fito waje cikin uniform na school, kallon kofansu hameed tayi tsaban tsinkewan zuciya har ta rame.
knocking akayi a hankali tace "ana zuwa"
zuwa tayi ta buɗe kofan, gani tayi ɗaya daga cikin masu aiki ne namiji rike da katon ghana most go yace "Allah ya taimaki ƴar sarki meenat wannan sakon ance na kawo miki naki ne"
ta kalleshi ta kuma kalli sakon da yace, tace "waye?"
yace "nima ban sanshi ba amma yace a kawo miki fuskanshi rufe yake"
tace "to na gode"
ɗauka zatayi taji da nauyi, gabanta yana faɗuwa taja zuwa ciki da kyar, buɗewa tayi dan ganin me aciki, idonta kamar zasu zubo bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yake rawa ta kwala ihu tace "ya kaseem? ya hameed? ku fito, ku tainakeni"
hameed ne ya fara fitowa, sannan sauran suka biyo bayanshi kallonta suke yadda take tsaye jikinta yana rawa ta kasa barin wajen, Ammi wacce itama ta gama ruɗewa da ganin ƴarta haka taje domin gani, ihu ta kwala tace "gawa"
hameed da kaseem sunzo a tare, kaseem ne ya kalla yaga kyakkyawar budurwa ce kwance yaga takadda a gefe, ɗauka yayi yaga an rubuta FAUZA da manyan harufa, kallon meenat yayi yace "fauza wacece ita? meyasa aka kawota nan?"
tana girgiza kai tace "ban sani ba yaya"
aneeta tana kallo ta rike hameed jikinta yana rawa cike da mugun tsoro tace "gawa hameed ba zan iya kallo ba a ɗauke anan"
ɓoye fuskanta take a jikinshi, mai martaba ganin abinda yake faruwa yace "kada kowa ya sani aje a binneta tunda bamu santa ba"
har yanzu jikin meenat bai daina rawa ba, fita da ita akayi, ammi tace "wai me yake faruwa ne damu?"
shiru suka zauna school ɗin da meenat bataje ba kenan, haka ta wuni da zazzaɓi da masifan ciwon kai, har dare tana kwance a ɗaki cikin bargo ta kasa fitowa, tunani ta fara, sai kuma ta tuna jiya data dawo kamar taji karan motsin buɗe kofa kuma tasan ba kofan ya kaseem bane, da sauri tace "Aneeta ya zama dole na bincike ta yanzu ma"
sauka tayi daga gadon ta fita a ɗakin, tana fita taga ta fito cikin sanɗa ta nufi kitchen, bin bayanta tayi taga tana tsaye ta juya baya a kitchen ɗin tana kallon hoto, a hankali ba tareda ta bari taji zuwanta ba taje ta bayanta ta tsaya, fige hoton tayi tana kallo, a razane tace "me haɗinki da ZEENAT LAMBA?"
juyowa tayi da jajayen idanunta tace "na san dama zaki biyoni kuma nasan kina bibiyata meenat"
tace "baki bani amsan dana tambayeki ba, me haɗinki da zeenat?"
murmushi tayi sai kuma tace "zeenat haka kawai babu respect? ba matar yayanki bace ita? da zaki kirata da sunanta gatsau"
tace "Aneeta baki bani amsa ba me haɗinki da zeenat?"
tace "sunana Aneeta lawan lamba ita kuma zeenat lawan lamba ina fatan kin gane me haɗina da ita?"
jikin meenat yana rawa tace "ki..ki...kina nufin ke...ke...kanwar zeenat ce?"
jijjiga kai tayi cikin rainin hankali tace "kwarai zeenat tsohuwar matar hameed ni kanwarta ce uwa ɗaya uba ɗaya ina fatan kin fahimta?"
jikinta yana rawa hoton ya faɗi, su biyu ne a hoton tana rungume da ɗayan ta baya sunyi hoton cikin nishaɗi, murya meenat ta ɗaga tace "A..Am..ammiii"
rufe mata baki tayi, kokarin kwacewa ta fara, ɗankwalinta ta ciro tana ɗaure bakinta suka fara kokawa, cikin muryanta dake cike da ban tsoro tace "kina nufin bansan abinda yake faruwa bane? fauza data kiraki jiya nice na kasheta sannan Amrah itama nice na kasheta, ki sani ba zan taɓa bari ki tonamin asiri ba har sai na gama duk abinda ya kawoni gidanku, zeenat wacce hameed ya kashe jininta ba zai tafi a banza ba, saina tarwatsa family ɗinku, saina kashe hameed kamar yadda ya kashe zeenat ya rabata da farin cikinta, dan rashin imani har yaron data haifa baku bari ba saida kuka haɗa da ita to ku sani ni kanwarta ce ta jini saina ɗau fansa, babu me yin rai a gidannan nayi niyan na barki ki kara wasu kwanaki a duniya amma ba zan taɓa barinki ba meenat"
ɗaureta tayi tana girgiza kai, ɗagata tayi ta fita da ita, kasancewar dare ne yasa ta fita ta kofar baya, a motan dake fake wanda itace ta ɓoye ta sata a ciki, shiga tayi itama taja motan da gudu ya bar bayan gidan, gudu take akan titi cikin iyawa, kamar zata bar garin saida ta iso wani babban ruwa sannan ta tsaya, kallonta tayi taga idonta a buɗe itama tana kallonta, murmushi tayi tace "karki damu watakila kinada tsawon rai shiyasa ba zan kasheki a take ba, amma dole zan rabaki da kowa naki"
fitowa tayi ta buɗe marfin motan ta ɗaukota, a cikin babban ruwan garin ta wurgata ba tareda ta kunceta ba, saida taga ta lume cikin ruwan sannan ta shiga mota ta koma gida, Allah ya taimaketa hameed bai tashi ba kuma babu wanda ya tashi a gidan kwanciya tayi a gefenshi ta rufe ido, cikin bacci taji ya riketa, rufe ido tayi tana jin wutan kinshi yana ruruwa a zuciyarta.


_Jiddah Ce....
 08144818849