SILAR MALAMINA: Labari Mai Ban Tausayi Dake Taba Zuciya

SILAR MALAMINA: Labari Mai Ban Tausayi Dake Taba Zuciya
 
 
*SILAR MALAMINA*
             ```Gajeren labari``` (1)
                        Na
*Hauwa'u Salisu* _(Haupha)_
 
Irin tashin hankalin da ƙadangaren da ya haɗiye kunama yake kasancewa a ciki, a irinsa Mubarak yake ciki; domin yana zaune ne a aji don rubuta jarrabawar shi ta ƙarshe; amma ya tattara dukkanin tunaninsa don nemo amsa haƙansa ya gaza cimma ruwa.
Idan an so yi masa rashin adalci, za a iya jefa shi cikin ɗaliban da ba sa karatu, amma a zahiri shi ya yi karatu iya yinsa sai dai ya gaza zama a kansa, kuma da ma tun fil'azal ba ya gane darasin Ingilishi. Da ya lura ba shi da wata mafita sai ya faɗa wa hau jirgi ya lula da shi duniyar tunani, ya tuna lokacin da yake sanar da abokinsa Muntasir matsalar shi ta tsoron jarrabawar Ingilishi, shi kuwa ya ba shi shawarar ya yi laya (satar amsa a takarda da ƙananan rubutu) ya shiga da ita. Shi kuma ya nuna masa ba zai iya ba, saboda yana tsoron kada a kama shi, don ya san hukuncin kora ne. Duk da ya ƙi karɓar shawarar sai da Muntasir ya rubuta masa wasu abubuwan a rigar shi, ya ce idan ta kulle ya rasa mafita sai ya kwafa.
Da wannan tunanin ya yi murmushi a ransa ya ce 'Dole na bi shawarar abokina, saboda ɓarawo ma da aka ce ka gudu cewa ya yi mutum ba ya ƙin ta mutane.' Da wannan tunanin ya yi shahadar ƙuda ya juya rigarsa ya fara kwafar abin da Muntasir ya rubuta ma shi.
"Hey! You stand up" 
Muryar Malamin da ke tsare su ta cika ajin, sai kowa ya kama kallon-kallo don ba wanda ya fahimci da shi yake.
 
Mubarak 'yan cikinsa suka juya nan take ya ji kamar ya ruga daga cikin ajin tsabar firgita ganin Malamin ya nufo in da yake, nan take jikinsa ya kama kyarma tamkar ɗan gangi, tuni ya yi sharkaf da gumi kamar wanda aka watsa wa ruwa.
 
Malamin ya ƙaraso ya kama rigarsa yana karanta abin da ya fara kwafa.
Nan kallo ya dawo kansu, masu dafe kai na yi masu kiran Allah na yi saboda kowa ya san matsalar Mubarak.
Mubarak Kamba ɗalibi ne mai hazaƙa da baiwa; amma a ɓangaren darrusan Hausa. Sai dai kuma duk yadda yake da ƙwaƙwar ya iya Turanci kamar yadda ya iya Hausa abin ya faskara, da ƙyar yake tsallake kowace jarraba ta Turanci, don babu wacce bai maimaita ba a dukkan jarrabawar Ingilishi da ya yi a baya.
 
Mubarak ya kama ƙafar Malam yana ba shi haƙuri da hawayensa yana cewa ya yaga takardar ya  ba shi sabuwar takarda ya sauya, amma ina, Malam ƙoƙarin cikewa Mubarak fom ɗin satar amsa yake yi.
Kaf ajin sun daina jarrabawar sun dage da ba wa Malam haƙuri amma ya yi kunnen uwar shegu da su ya cike wa Mubarak fom ya kai hukumar makaranta.
Ya dubi Malam Zubairu  yana kuka ya kama ƙafar shi ya ce, "Don Allah kar ka zama silar wargajewar rayuwata da ta ahalina, mahaifina ya rasu ina da ƙanne maza da mata da nauyinsu ya rataya a kaina, mahaifiyata ba ta da cikakkiyar lafiya idan ta ji an kore ni komai zai iya faruwa da ita, don Allah ka taimaka min ka taimaki rayuwar mutanen da ke ƙasana, ban san in da zan nemi kuɗin da zan sake dawowa karatu ba. Wannan ma na ƙarshen bashi mahaifiyata ta samo min na biya, Malam kar ka tarwatsa min rayuwa don Allah!
Malam Zubairu ya kalle shi ya kanne ido na azabar masifa ya ce, "Ba ruwana da wata rayuwarka, ka san da hakan ka saci amsa? To wallahi duk makarantar nan ban ga wanda zai hana a kore ka ba."
 
Innalillahi kawai Mubarak ke maimaitawa, nan take ya fice hayyacinsa kamar ba shi ba, ya zama abin tausayi amma ko a jikin Malam Zubairu sai ma zuwa ya yi da ya cike fom ɗin da za a ba shi kayan da ake ba duk Malamin da ya kama mai satar amsa da ya yi yana murmushi.
 
Ga alama jikin sauran Malaman ya yi sanyi amma ban da na Malam Zubairu, ko a kwalar rigarsa haka ya miƙa wa Mubarak Form ɗin kora. Nan take duk da sauran Malaman sun ce a bar shi ya zauna tun da ko layin farko bai kai ba na rubutun da ya fara yi ba, asalima abin da yake rubutawa ba shi ne amsar tambayar da akai ba, amma Malam Zubairu ya ce ba ruwansa shi dai doka ya bi don haka ya kama mai satar amsa a kore shi kawai shi kuma a ba shi kayan da aka tanada ga duk wanda ya kama mai satar amsa.
 
Ba wanda ya so abin da Malam Zubairu ya yi amma ya suka iya, suna ji suna gani ya kori yaron.
 
Mubarak kamar mahaukaci haka ya dinga bin Malamai amma ina ba mai wannan damar dama guda ce ta gun Malam Zubairu kuma bai amfani da ita ba don haka sai dai suka ba shi haƙuri kawai, haka ya fice daga makarantar kamar mahaukaci ya nufi ƙauyensu ko kayansa bai ɗauka ba.
 
 
Allah Ya sa ma akwai kuɗi aljihunsa ya biya ya isa gida har zuwa lokacin kuka yake sosai kamar wata macen da mijinta ya mutu a gabanta kan gadon asibiti.
 
Yana faɗawa gidansu ya zube gaban mahaifiyarsa da ƙannensa ya dafe kansa ya ci-gaba da kuka mai sauti nan take hankalinsu ya tashi ainun saboda ba su taɓa ganinsa a irin yanayinba, Mubarak nada dakiya da danne damuwa ba kowa ke iya gane damuwarsa ba lokaci guda ba, amma shi ne a wannan yanayin Yau, tabbas akwai yadda akai.
 
Hannun mahaifiyarsa ya kama yana kuka yana bata haƙuri bakinsa ya kasa bayyana abin da ya faru sai haƙurin da yake ba mahaifiyar ta shi wadda ta gama ruɗewa baki ɗaya, sai girgiza shi take tana tambayar me ya faru.
 
"Mama ki yafe min nayi laifin da aka koreni daga makaranta kwata-kwata a Yau amma wallahi ba da san raina ba, ban da yadda zan yi ne Mama don Allah... Maganar ta datse ne ganin mahaifiyar ta shi ta sulale daga yadda take zaune zuwa kishingiɗe miyau na zubowa ta gefen bakinta numfashinta na niyyar ɗaukewa baki ɗaya.
 
Da gudu suka kwasa shi da ƙannensa zuwa waje neman mai motar da zai kai su asibiti amma ba kowa wajen ba mai ko Napep da ya biyo ta gun, hakan yasa Mubarak shiga makwaƙtansu da gudu neman taimakonsu. Tare suka shiga gidan zuwa lokacin bata ma san waye a kanta ba tsagin jikinta ya shanye baki ɗaya ta koma kamar ba ita ba.
Da ƙyar aka samu mai motar da ya ɗauke su zuwa asibiti, nan take aka kai ta emergency room aka buƙaci dubu ashirin da biyar da za a fara duba ta, amma ban da Naira ɗari biyu ba komai a cikin aljihun Mubarak. 
Kuka mai cin rai ya ƙwace mai a karo na barkatai yana kiran sunan Allah da neman ɗauki a gunshi.
Da gudu ya koma gida amma ba wani abu na kirki da za a ɗaga a saida wanda ya kai ko da darajar dubu goma ne a cikin gidan, saboda komai nasu ya ƙare karatun shi ma rabi duk da kuɗin bashi yake yinsa sai a hankali shi da mahaifiyarsa ke biya ta hanyar dako da yake shiga cikin gari yana yi ita kuma tana wanki da guga. 
 
Hakan yasa ya sake ficewa cikin gari neman bashi amma bai samu ko sisi ba, dole ya koma asibitin ya iske ta yadda aka kai ta haka take kwance akan gadon ba abin da akai mata saboda bai ba da kuɗi ba, sai ma faɗa da Malaman asibitin ke yi ya kawo masu marar lafiya ya aje ba ko sisi to ya ɗauke ta ba su da wajen ajiyar mutane su haka nan.
 
Da ƙyar ya samu mai Napep ɗin da ya ɗauke su zuwa gida akan Naira ɗari biyun nan dake aljihunsa.
Sai da suka kwana goma cikin mugun tsanani da rashin ci da sha sai dai su roƙo a maƙwabta, ita kam Mama sai dai a ɗura mata koko ko fura tana kwance ba ta iya komai na tsawon wannan kwanakin.
 
Mubarak duk duniyar tai mai zafi, ya rasa mai ke mai daɗi baki ɗaya komai ya fice mai a ransa kawai fatansa ya samu kuɗin da zai kai mahaifiyarsa asibiti amma kullum da ƙyar yake samun abin da zai ci da kansa da ƙannen nasa. Ko da yaushe yana zama ya sha kuka har ya ji ba daɗi.
Idan akwai abin da ya tsana a rayuwarsa to karatun jami'a ne yanzu, ya tsani karatun ya tsani masu koya karatun ji yake zai iya kashe Malamin jami'a idan ya samu damar hakan musamman Malam Zubairu.
 
Kwatsam! Ranar wata juma'a yana kasuwa yana yin dako ya ɗaukar ma wani saurayi kaya zuwa cikin mota ya saka mai a bayan mota yana jiran ya ba shi kuɗin aikinsa yaga sai kallonsa yake kamar ya san shi, hakan yasa ya sadda kansa ƙasa kasancewarsa marar san magana daman can.
 
"Ya sunanka? Cewar saurayin.
 
Mubarak ya kalle shi da alamar mamaki a fuskarsa ya yi shiru saboda bai ga amfanin tambayarsa suna ba. Hakan yasa ya yi shiru bai tanka ba sam.
 
Matashin ya sake tambayarsa "Ya sunanka don Allah, naga kamar nasanka ne amma na manta inda na sanka don haka na tambayeka."
 
Mubarak ya ja ajiyar zuciya ya ce, "Gaskiya ban sanka ba baka sanni ba, sunana Mubarak Yau ne na farko da na fara ganinka a rayuwata."
 
Matashin ya yi murmushi sosai ya ce, "Haka ne amma dai ka birgeni sosai da kake neman na kanka baka sa ma kanka girman kai ba gaskiya... Zuwan wani matashin yaro yana haki gunsu da gudu yasa ya dakata da maganar da yake yi.
"Yaya ka zo ka ga yadda Mama ke yin wani abu tun ɗazun! 
Da gudu ya kama hannun yaron suka juya suka bar matashin a tsaye, hakan yasa ya shiga motarsa ya bi bayansu da hanzari, ya leƙo ta tagar motar ya ce "Ku zo na kai ku gidan." 
Ba musu suka faɗa motar ƙanin ke gwada mai hanya don shi Mubarak ya nausa duniyar tunani ma bai san  abin da ake yi ba.
 
Ko da suka iso ƙofar gidan sai da matashin ya taɓa shi sannan ya zabura ya buɗe motar ya afka gidan dama ba ko ƙofa shima bai jira komai ba ya bi bayansu zuwa cikin gidan.
 
Ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba ganin yadda shi kanshi gidan nasu yake ba, kamar ba mutane ke rayuwa a ciki ba, amma dai ya lura da akwai tsabta sosai a cikin gidan don ba ƙazanta sai dai tarin talauci da ya mamaye gidan da mutanen gidan daga ganin tsarin gidan kasan komai ya tsaya ga mutanen gidan ba wata rayuwa ta farin ciki a gidan sai godiyar Allah.
 
Lokacin da ya yi ido huɗu da matar da ke kwance sai da ya razana ganin jikinta rabi ya shanye ga yara mata biyar zaune da maza uku duk sun zagaye ta sai kuka suke shi kam Mubarak ɗin ma bango ya dafe ya ci-gaba da raira kuka kawai.
 
Cikin sauri ya nufi Mubarak ɗin ya ce, "Mu je a kaita asibiti zaman me kuke da marar lafiya a cikin gida, ga ciwo ya yi tsanani? 
 
Ko motsi Mubarak bai ba, don bai da kuɗin da zai biya ko an kai ta, don haka ya ci-gaba da kukanshi kawai jikin bango.
 
Sai da ya daka mai tsawa sanan ya dube shi ya ce, "Da me zamu kai ta asibitin bayan ba mu da ko sisi ?"
 
Matashin ya girgiza kai ya ce, "Ba lokacin wannan maganar mu je kawai a kaita mun zanta daga baya."
 
Haka suka ɗauki Mama zuwa asibitin dake cikin gari da gani na kuɗi ne saboda tun daga waje komai yake a kammale ga shuke-shuke masu kyau an yi a harabar asibitin, suna tsayawa aka fito da gadon ɗaukar marassa lafiya aka ɗora Mama bisa akai ciki da ita.
 
Waje suka samu suka zauna sai raba idanu suke kamar a ce kar su ruga.
 
Suna ganin yadda ake ta shige da fice a ɗakin da aka shigar da Mamar, su dai ba mai magana duk sun zuba ma sarautar Allah ido kawai. 
 
An ɗauki lokaci sannan likitocin suka fito daga ɗakin aka ce mutum ɗaya ya je, Mubarak da saurayin suka kalli juna sai Mubarak ya ce, "Kai ka kawo ta don haka kai ya kamata ka je."
 
Hakan yasa matashin bin bayan Likitan kai tsaye.
 
Ya jima sannan ya fito hannun Mubarak ya kama suka fice kai tsaye mota suka shiga ba su zame ko'ina ba sai wani makeken shagon kayayyaki, matashin ya shiga ya dinga kwasar kaya  shi dai Mubarak bai taɓa komai ba iyakarsa bin matashin kawai da idanu yana mamaki.
 
Sai da ya suka cika bayan motar da kayan abinci iri-iri sannan suka tafi ya sai mai fari da ja na girki da magi kala-kala sannan suka nufi garinsu Mubarak kai tsaye yai parking a ƙofar gidan ya ce ma Mubarak ya taya shi su shiga da kayan cikin gidan. 
 
Shi kam Mubarak mamaki ya cika mai zuciya sosai kan lamarin matashin da ko sunansa bai sani ba.
 
 
Ƙannensa mata saurayin ya kalla ya ce, "Ga kayan abinci nan ku samu abin da kuka dafa naku kaɗai na asibitin can a san abin da aka samu. Duk jikinsu ya yi sanyi basu san ko waye ba sun dai ga ya shigo kawai amma sai hidima yake masu kamar shi ma ɗan gidan ne.
 
Mubarak ya zuba mai ido ya rasa abin da zai ce mai saboda shi ya kasa fahimtar abin da ke faruwa ma sam.
 
Haka dai suka sake komawa cikin gari asibitin da aka kwantar da Mamar har ta samu barci kamar ba ita ba jiki ya fara samun sauƙi.
 
Nan ma bai zauna sai da ya cika ɗakin da kayan ƙwalama iri-iri ba abin da babu a cikin ɗakin.
 
Waje suka fito bayan sun ɗauko abincin da bai san inda ya siyo shi ba suka koma inda ba mutane suka zauna kan kujerun da aka aje don zaman mutane.
 
Matashin ya dubi Mubarak ya yi murmushi ya ce, "Sunana Ayuba tun da ba zaka tambayeni ba, duk da ban san dalilinka na hakan ba Mubarak. Dr. Ya bayyana min cewa mahaifiyarka na fama da ciwon hawan jini wanda sanadin ɓacin rai da take fuskanta yasa ya yi mata yawa a cikin jikinta, sanadin taga wani abu da ya ɓata mata rai ya razanata yasa nan take jininta yai sama sosai har ya taɓa mata rabin jikinta da idanunta, amma dai Dr. Ya tabbatar min da cewar za su yi bakin ƙoƙarinsu don ganin ta samu lafiya ba da jimawa ba, don za su dinga yi mata gashin ƙashi yadda ya kamata da duk wata kulawa."
 
Mu haɗu a kashi na biyu.
Taku: Hauwa Salisu (Haupha)