ƘADDARA TA: Fita Ta Biyar

Abbi dake tsaye yana jin kanshi da nauyi ya lumshe ido a wahale ya buɗe yana kallonta ta ɗau bindigan, sultan ne yaje ya rungumeta ya kwace bindigan yayi wurgi dashi, tace "sultan mutuwana shine alkhairi, sultan komai baya tafiya daidai komai baya gyaruwa sai daɗa ɓaci yake, sultan watakila idan na mutu komai zai daidaita" kanƙameta yayi yana shafa bayanta yace "shiru ammi"

ƘADDARA TA: Fita Ta Biyar


ƘADDARA TA


        Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 5*


                  ~Babu abinda yake cin ranshi kamar maganan dake bakinshi wanda ba zai iya faɗanshi ba, Abi ganin haka yazo da sauri zai taɓashi yayi baya yana girgiza kai alaman baison kowa ya taɓashi, Abi yace "hameed dan Allah kayi hakuri"
juyawa yayi a fusace yaje wajen kaseem, bindigan ya kwace ya saita kanshi, waro ido kaseem yayi ganin yana huci yana shirin harba bindigan, Aneeta cikin tashin hankalin da tunda mama da baba suka haifeta bata taɓa gani ba tace "dan Allah kada ka kashe kanka dan Allah"
ya kaseem yace "hameed kada kayi wannan kuskuren wallahi idan ka kashe kanka shima saina kashe shi"
hawaye ne suka fara wanke mishi fuska ga magana amma babu bakin faɗa, ganin da gaske yake kaseem ya buɗe drower dake bayanshi kusa da tv, ciro bindiga yayi ya nufi waje, a kiɗime ammi tace "kaseem ina zakaje?"
juyowa yayi ya kalli hameed yace "kina ganin idan hameed ya mutu zan kyaleshi ne? kafin ya kashe kanshi saide su mutu a tare"
hameed bindigan yasa hanu a kunaman ya harba, Aneeta da tazo da gudu ta rungumeshi ta wurgar da bindigan gefe kafanta bullet ɗin ya sama, kara tayi cikin azaba ta kanƙame hameed da suka zube kasa tare, akanshi ta faɗi hakan yasa ya rike waist nata sosai idonshi a rufe, jigidan dake waist ɗinta yaji hanunshi a kai, cikin kuka tace "kafata"
kaseem ne ya wurgar da bindigan yazo da gudu ya ɗagata yana duba kafarta dake jini, ammi hawaye ta share tace "shikenan tunda nice yanzu abin zargi kowa ya manta da laifinshi wanda aka lulluɓe sabida muninshi kafin ku kashe junanku ni bari na kashe kaina"
Abbi dake tsaye yana jin kanshi da nauyi ya lumshe ido a wahale ya buɗe yana kallonta ta ɗau bindigan, sultan ne yaje ya rungumeta ya kwace bindigan yayi wurgi dashi, tace "sultan mutuwana shine alkhairi, sultan komai baya tafiya daidai komai baya gyaruwa sai daɗa ɓaci yake, sultan watakila idan na mutu komai zai daidaita"
kanƙameta yayi yana shafa bayanta yace "shiru ammi"
kuka take yi, kaseem ne ya rike aneeta ta zauna akan sofa tana ciza baki cikin hawaye, ɗaki ya koma ya ɗauko kayan aiki yazo ya fara cire mata bullet ɗin, tashi hameed yayi ya zauna a gefe yayi shiru yana kallon yadda take ciza baki tana rufe ido, cire mata yayi, rikeshi tayi tana ihun zafi, minat tace "sorry"
shima cikin sanyin murya yace "sorry"
saida ya tabbatar jinin ya tsaya kafin yayi dressing wajen, a hankali ya tashi yana kallonta zubewa kasa yayi ya haɗa hanu biyu yace "thank you, na gode sosai da kika ceci rayuwar hameed na gode"
raba hanunshi tayi tace "ka daina min godiya ba kunce mun zama ƴan uwa ba?"
cikin kuka yace "na gode"
tace "ka daina yafi karfin komai a wajena kune kuka taimakeni kuma zan iya taimakonku a koda yaushe matukar zan iya"
a hankali ya tashi, Abi waya ya kira babu jimawa wasu maza suka shigo gawan ya nuna musu cikin bala'in ciwon kai da nauyin da kanshi yayi yace "kuje ku binneta ku ɓoyewa kowa kada kowa ya sani"
amintattunshi ne suna iya ɓoye komai wanda ya shafeshi matukar yace musu su ɓoye koda baice su ɓoye bama ɓoyewa suke bale yace su ɓoye, fita da ita sukayi ta kofan baya, aneeta binsu tayi da kallo har suka fita suka rufe kofan, bata taɓa sanin akwai kofa a wajen ba sai yau da taga sun buɗe domin ɓoye sirri, tashi hameed yayi ya fara tafiya fadeel ne ya rikeshi yace "yaya bari na kaika ɗaki"
ɗakin ya kaishi ya zauna kawai akan gado yayi shiru, fita yayi, minat ce ta taimakawa Aneeta suka tafi ɗaki, ammi ma sultan ya kaita ɗaki, abi yana rike da kanshi ya wuce fada, har zazzaɓi yake ji baisan meyasa ba kullum lamarin gidanshi ɓaci yake, babu abinda yake tafiya daidai.

Aneeta tana kwance tana kallon minat tana kuka, shiru tayi dan ta kasa gane meke faruwa a gidan, cikin sanyin murya tace "kiyi hakuri ki daina kuka komai yayi zafi zaiyi sanyi Insha Allah"
share hawaye tayi tace "babu abinda zaiyi sanyi a wannan gidan babu shi aneeta komai kara lalacewa zaiyi babu abinda zai dawo daidai"
shiru tayi tana kallonta, sai kuma tace "amma kada nayi shishigi waye ya kaseem yace zai kashe?"
shiru tayi kamar ba zata amsa ba sai kuma tace "wani ne"
tace "wanene shi?"
girgiza kai tayi tace "wannan sirrin gidan sarautarmu ce, wannan sirrin babu wanda ya sani sai mu kaɗai ƴan gidannan kuma alƙawari ne babu wanda zaiji"
tace "to shikenan Allah ya daidaita komai kiyi ta addu'a"
tace "insha Allah"
duk yadda taso tayi bacci ta kasa abinda ya faru yau ya tsaya mata a wuya data rufe ido yarinyar take gani a kwance, kenan suna iya kisa kuma su kwana lafiya? tsoron gidan ma ta fara fitsari takeji amma ta kasa tashi taje tayi haka take kwance data motsa kaɗan sai taga kamar zasu harbeta itama, kuma tasan babu abinda zai faru idan ta mutu, tashi tayi tace "anya aneeta ba zaki nemawa kanki hanya ba? anya ba gudu zakiyi ki bar gidannan ba?"
kallon minat dake bacci tayi sai kuma ta kalli kofa, cikin sanɗa ta sauka daga gadon ta manta ma da zancen hijabi kawai ta nufi hanya ta fita a ɗakin, cikin sanɗa take tafiya duk gidan duhu ne sabida an kashe wutan, wannan al'adansu ne idan zasuyi bacci su kashe wuta, cikin gudun tayi tuntuɓe ta zube a kasa kara zatayi tayi saurin rufe bakinta da hanu, tashi tayi zata tafi taji kamar ana bubbuga kofa da sauri ta kalli kofan da ake bubbugawa taga kofan ɗakin hameed ne kamar zata tafi sai kuma wani abu yace ta tsaya ta duba menene, a hankali ta buɗe kofan ta shiga, taka mutum tayi ta waro ido a firgice zata kwala ihu taga hameed kwance a kasa yana birgima, da sauri tace "hameed? meyasa sameka?"
hanunshi ya mika mata da sauri ta rike hanun, taɓa jikinshi tayi taji da zafi sosai, cikin tsoro ta taimaka mishi ya tashi, da kyar yake ciza baki yana runtse ido, takalmin data rike a hanu ta zubar ta zauna a bakin gadon ta taimaka mishi ya kwanta, tace "me yake damunka?"
hanunta ya rike a razane ta kalleshi ganin ya cusa hanunta a cikinshi, zata kwace hanun ya damƙe da nashi, shiru tayi jikinta yana rawa ta kasa ɗauke idonta akanshi, gani tayi yana lumshe ido tareda kara tura hanunta cikin jikinshi, fizge hanunta tayi cikin tsoro ta tashi zata gudu dan bata taɓa ganin abu haka ba a rayuwarta, fizgota yayi ta faɗo jikinshi baki ta buɗe zatayi ihu ya toshe bakin, waist beads nata da yaji ɗazu ya fara wasa dashi, ganin tana kanshi idanunta sun kara girma sosai ba kaɗan ba, kwace kanta take ya kara danneta a kanshi yana kara wasa da waist beads ɗin, da kyar ta samu ta zame hanunshi daga bakinta zatayi ihu ya haɗa bakinshi da nata, cikin tashin hankali take bugunshi da karfi tana hawaye, wuntsila kafafunta takeyi tana neman hanyan tsira, so yake yace mata ta nutsu babu abinda zaiyi mata amma babu bakin magana, tun tana iya fizgewa har jikinta yayi sanyi tayi shiru kawai tana jinshi, a hankali ya zame bakinshi daga nata, juyar da ita yayi ta kwanta a gefenshi numfashinshi ke sauka akan dogon wuyanta, hanunta ya rike wanda ta kasa ko ɗagawa yasa a maranshi yana shafawa, jikinta har yanzu bai daina rawa ba, kuka take yi sosai kuma ta kasa magana, saida taji yayi shiru kafin ta faki idonshi ta dira a gadon da gudu zata fita a ɗakin, baya tayi a razane ganin ya kaseem daya shigo yanzu, da waya a hanunshi, kallonta yayi sai yaga ta sunkuyar da kai jikinta yana rawa, kallon miss calls ɗin da hameed ɗin yayi ta mishi yayi yau bacci ne ya saceshi shiyasa baiji kiran ba, baiyi magana ba itama batace komai ba, yace "jeki"
raɓawa tayi ta gefenshi ta wuce a guje, kallon hameed daya lumshe ido kamar me bacci yayi, karasawa yayi ciki ya zauna a bakin gadon yana kare mishi kallo, lips nashi da sukayi pink sosai ya kara kallo sai kuma ya kalli kofan yace "tashi kasha magani"
make kafaɗa yayi alaman no, cikin tsawa yace "tashi mana"
tashi yayi yana yamutsa fuska, ya bashi ruwa da maganin yace "sha"
buɗe baki yayi yasha maganin yana rufe ido, kwanciya ya kuma yi yana kokarin rufe kanshi da blanket ganin yadda kaseem ɗin yake kallonshi, ya rike blanket ɗin yace "me kayi mata?"
shiru yayi yana turo karamin bakinshi, yace "me kayi mata nace?"
yasan bazai iya amsawa ba amma tsaban haushi yasa yake mishi tambayan, tsawa ya daka mishi yace "me kayi mata nace?"
a hankali ya ɗaura hanu akan lips nashi ya shafa, kaseem yace "kiss?"
gyaɗa kai yayi, yace "kenan ba zaka iya hakuri ba idan kana ji bakasha magani ba? shine har zakayi kokarin raping mace?"
girgiza kai yayi da sauri alaman ba raping nata yayi niya ba, tsaki yaja yace "hameed na rasa wani irin jaraba ne da kai sam bakada hakuri ko kaɗan bakasan a matsayin kanwarka take bane?"
kanshi kasa yaki yadda su haɗa ido, ya kara jan tsaki yace "to Allah ya shiryeka ko ni da nake yayanka na girmeka nesa ba kusa ba banada wannan masifan jaraban"
tafiya zaiyi ya rike mishi hanu, ya juyo yace "me kuma?"
lumshe ido yayi, tsaki yaja shifa ya fara gajiya da lamarin hameed sai shegen lumshe ido kamar mace, yace "me kake so?"
wayanshi ya karba ya fara typing, mika mishi yayi ya karanta (Aneeta nakeso)
da mamaki ya kalleshi yace "to ai ba matarka bace ba yadda za'ayi tazo ta kwana anan"
lumshe ido ya kuma yi ya kara typing (ka auramin ita)
murmushi yayi bayan ya karanta kawai ya fita daga ɗakin ya rufe, Aneeta nunfashi take saukewa da kyar bayan ta koma ɗakin ta laɓe a bayan minat, a mugun tsorace take da gidan da kaseem harma da hameed wanda ya mata abinda bata taɓa zaton zaiyi ba yau, kuka ta fara tace "aneeta kin shiga uku baki lalace ba"
minat da tayi kamar tana bacci dariya takeyi sosai sabida itace ma taje ta kira ya kaseem tunda ta fita taji karan kofa tabi bayanta har zuwa lokacin daya kaseem ya shiga ɗakin kafin ta dawo ta kwanta.

haka har tayi kwana biyu a gidan bata yadda ta fito idan yana falo shima bai damu ba yasan idan ta gaji zata fito da kanta, a rana na uku minat ce ta sata dole ta fito sanye take da bakin dogon riga tayi kyau sosai fuskanta ya kara yin haske da kyau, zama tayi a kujeran dinning ta gaida Abi sannan ta gaida Ammi dasu kaseem, harda sultan ta gaishe sannan ta saci kallon hameed dake cin abinci bai ko kalli inda take ba, a hankali tace "ina kwana"
gyaɗa kai kawai yayi kamar ma baisan da ita ba, kaseem ya kalleshi sannan ya kalleta yaci gaba da shan tea, mai martaba daya gama yace "Alhmdllh, Aneeta"
da sauri tace "na'am Abi"
yace "zan haɗa aurenki da hameed"
ba ita ba har ammi da minat saida suka kaɗu da jin maganan, da kallo ammi ta bishi, kaseem yasan da maganan shiyasa bai damu ba, aneeta cikin bashi girma tace "to Abi"
yace "kina sonshi?"
shiru tayi tana kallon hameed dake cin abinci bai kalleta ba, yace "kina sanshi?"
wasa take da yatsun hanunta a hankali ta gyaɗa kai, murmushi sultan yayi yace "wow abu yayi kyau"
tashi Abi yayi yace "juma'a me zuwa aurenku saura kwana biyar kenan"
tafiya zaiyi ammi tace "mai martaba"
tsayawa yayi yana kallonta, tace "kamata a tabbatar tana sanshi kada a cutar da ɗaya"
yace "gashi ta amsa shima da kanshi yace yana sonta"
tana kallonshi tace "amma ai batasan komai ba"
mai martaba ya ɓata rai kamar bai taɓa dariya ba, tace "ni ba zan bari a cutar da mutum ba, ya kamata tasan cewar Abdulhameed ya taɓa aure...."
wani irin tsawa kaseem ya daka mata, shiru tayi tana kallonshi yace "ko sau ɗaya ko sau ɗaya ki zama...."
tace "karka kuskura ka gayamin magana kaseem sabida kafin kowa sanin abinda yake faruwa, sannan kai kanka kasan cutarwa ne ayi aure da ɓoye ɓoye"
cikin haushi da ɓacin rai da yake ciki yace "me amfanin tuna baya?"
tace "sabida kasan duk bamu aikata mai kyau ba?"
yace "kece dai amma ni..."
tace "amma kai me? kai mutumin kirki ne kaseem? bakayi komai ba? kafi kowa sanin auren hameed ba karamin tashin hankali zai tono ba kafi kowa sanin irin masifa da bala'in da za'a shiga matukar hameed ya samu sarautan yarima kuma yayi aure kafi kowa sanin abinda zai faru..."
buga kujeran yayi kamar zai ɓalla, saida abincin dinning ɗin duk suka zube, yana kallon cikin idonta yace "me zai faru? me zai faru nace idan hakan ya faru?"
dariyan bakin ciki tayi wanda kana gani kasan ba har cikin ranta tayi ba, tace "ina fatan baka manta cewar ABDULHAKEEM bai mutu ba yana raye......"
kamar zai fasa kunnuwansu yace "ya mutu zuwa yanzu ya mutu a inda yake baya raye"
itama kamar zata fasa kunnuwansu tace "Abdulhakeem...."
ihun da aneeta tayi yasa suka kalleta babu shiri, tana rike da hameed daya yanka jijiyan hanunshi yana zubar da jini kamar jikin jikinshi zai kare, ammi ce ta kwala ihu taje da gudu zata taɓashi kaseem yace "stay away from my brother"
yayi maganan cikin tsananin ɓacin rai, kasa taɓa hameed ɗin tayi sai rawa da jikinta yake, kaseem yana hawaye yace "idan ya mutu shikenan? duk zaku huta idan ya mutu?"
zama yayi akan kujera ya harɗe hanu a kirji yace "to shikenan Aneeta barshi ya mutu, watakila komai ya dawo daidai idan Abdulhameed ya mutu"
yana maganan yana hawaye me zafi, yace "amma ki sani"
ya nuna ammi yace "wallahi idan Abdulhameed ya mutu ko Abdulhakeem bai mutu ba saina kasheshi nayi alkawari"
zata taɓashi cikin tashin hankali ya kara daka tsawan da yasa jikin aneeta fara rawa yace "don't dare touch him Ammi"
cak ta tsaya, mai martaba kirjinshi ya rike yana jin jiri, kasa tim ya faɗi kaseem yana kallonsu babu abinda yayi sai naɗe hanu da yayi a kirji, yana kallon sultan dasu fadeel suna ihu, masu tsaro ne suka shigo jin ihu da wani irin tsawa kaseem yace su fita, jikinsu yana rawa suka fita, aneeta tana ganin jini yaki tsayawa ta sauke kanshi daga cinyarta daya gama ɓaci taje gaban kaseem ɗin ta durkusa, kafanshi ta rike cikin tashin hankali tace "dan girman Allah ya kaseem dan girman Allah ka taimaki hameed idan ya mutu ban san yadda zanyi ba, dan Allah ka taimakeshi jininshi yana gab da karewa"
ɗauke kai yayi ya juya yana kallon gefe yace "Aneeta ki barshi ya mutu"
ganin ba zai kulata ba taje da gudu ta cire ɗankwalin kanta ta ɗaure hanunshi dake jinin gam, janshi tayi a kasan zuwa kan sofa, kankara ta ɗauko a fridge tazo da gudu kamar mahaukaciya manna mishi tayi a hanun sabida ya daskarar da jini, tayi sa'a jinin ya daina gudu sosai ya ɗan tsaya, ta sauke kanshi daga cinyarta ta ɗaura akan sofan ta haura sama da gudu, first-aid-box ta ɗauko da sauri ta dawo ta ciro audiga da bandage kamar yadda taga anayi ta fara dressing ciwon, cikin sa'a Allah ya taimaketa hanun ya daina jini, tashi tayi ta fita ta kira driver taje asibiti, yaki shigowa da kanta ta ɗagashi ta fita dashi, sai nishi take sabida wahala, a mota suka tafi asibitin ya kaseem ɗin, suna ganinshi suka fara taimakonshi da gaggawa, Allah yasa suka ɗinke ciwon, yana kwance akan gadon tana zaune a gefenshi ta haɗa kanta da jikin gadon tana kuka, a hankali ya buɗe ido yana jin sautin kukanta, ji tayi ya rungume waist nata ya manna kanshi da bayanta, shiru tayi ta share hawayen, a hankali ta juyo gaba ɗaya ta yadda zaiji daɗin hugging ɗinta, a hankali ya matso sosai ya manna kanshi da kirjinta yayi shiru, shafa kanshi tayi cikin jin daɗi tace "Alhmdllh baka mutu ba na gode Allah"
murmushi taga yayi, hanunta ya rike yana kara cusawa a kanshi, cikin farin ciki taci gaba da wasa da gashinshi, lumshe idonshi kawai yayi.
turo kofan akayi ya kaseem ne ya kasa zama duk yadda yaso ya bari hameed ya mutu ya kasa yin hakan, da sauri ta ture kanshi yaki sakinta sai daɗa kanƙameta da yake, cikin jin kunya tace "sannu ya kaseem"
hawaye yake yi yana jin kunyan haɗa ido da kaninshi da ɓacin rai ya hanashi taimakonshi yace "ke zan yiwa sannu aneeta gaskiya sai yanzu hankalina ya kara kwanciya idan kika yadda kika aureshi zanfi samun nutsuwa"
a hankali tace "karka damu babu abinda zai hanani auren yarima hameed saide idan kaine ka hana ko kuma shi yace bayaso"
yace "na gode"
kallon hameed daya lumshe ido a jikinta yayi sai kuma ya kalli hanun dake ɗaure da bandage, yace "sannu hameed"
gyaɗa kai kawai yayi yana kara kanƙame waist na Aneeta, tureshi takeyi ta kasa sakin jikinta duk a takure take, ganin haka kaseem yace "ina zuwa"
fita yayi, da sauri tace "baka ganin ya kaseem ne?"
shiru yayi mata, sun wuni a hospital ɗin sai dare kafin kaseem yazo yace su tafi, tafiya sukayi suna shiga gida kaseem yace "sultan ya jikin Abi?"
yace "da sauki ammi tana can wajenshi"
yace "Allah kara mishi sauki"
sukace "ameen"
sukace "sorry ya hameed"
lumshe ido kawai yayi ya wuce ɗakinshi.

_jiddah ce....
 08144818849