ANA BARIN HALAL...: Fita Ta Shida
ANA BARIN HALAL...:
*STORY AND WRITTING BY AUNTY NICE*
*BISMILLAHI RAHMANIN RAHIM*
*PAGE* 6
Bayan gama bikin Jamila da 1week suka bar ƙasan da mijinta zuwa london, Allah sarki har gidanmu tazo ta mana sallama da yammah ita da mijinta, lokacin da muka fito rakata wurin motan ta riƙo hannu na muka ɗan tsaya tana dubana, "Ɓesty kim san yayah Aliyu ya birkece akan ki kuwa? Duk tsare gidan shi amma sai da ya sake ya sameni da maganan, yana ta tambaya na akwai wanda yake neman kine ko yayah ake ciki? Ni dai nace mishi for now babu kowa sai burin fara karatu da kikeyi, nagaya miki mummy sai farin ciki ta ke tayi, yanzu haka ma ya koma lagos kin san achan yake aiki, ya tambayeni number wayanki nace har yanzu de baku fara riƙewa ba", ta sake damƙe hannu na fuskanta cike da jimami tace, "Besty gashi zan tafi na bar ƙasan ban san yayah zanyi da ke ba, nasan hala idan baki ganin ido na kiƙi amsa yayah na, don nafi kowa sanin baki son baƙi, Besty yayah na fa bawai baƙin har chan bane, gashi mai ilimi da class", ta faɗa kaman zata mun kuka.
Juya ido nayi ina kallon ta, "Besty nifa bawai baƙine bana so ba, nifa ban kai aure ba, karatu nake son yi, kuma.... Sai nakasa ƙarasa faɗin abun da zan faɗa na ƙura mata ido.
"kada ki damu besty insha Allahu komai zai tafi daidai indai har muna tare" maryam ta faɗa tana dafa kafaɗan jamila, ni dai ido na bisu ban sake cewa komai akan maganan yayan ta ba, bayan sun tafi muka wuce raka maryam gidan su.
Maryam sai bayani takeyi akan haɗuwan Aliyun, amma ita tsoronta jujuna, nidai ko kulata banyi ba.
Wannan dawowan Abban mu daga Abuja ya taho mana da waya masu shegen kyau da tsada, murna nida habiba kaman babu gobe, a lokacin hafsy take turo baki gaba tana, "Abba mu fah? Muma fah muna son wayan Abba", Abba yace, "Yayanku Ahmad ne ya bayar aka wo musu, dama ya musu alƙawarin idan sun gama school result ɗinsu yayi kyau zai saya musu waya, kuma Alhamdulillahi abu yayi kyau, kuma ku dage ku maida hankali akan karatunku, idan kun gama za'a saya muku".
Mudai sai murna mukeyi muka miƙawa su ummi domin su saka mana albarka, murmushi ummi tayi tace angode wa yayan su Allah ya bar zumunci, sannan ta mana nasiha akan riƙe waya da muka jin tsoron Allah, mamah ma nasihan ta mana, sannan ta mana murnan wayan, sannan ta maida hankalinta kan su Raliya tana musu faɗa akan komai aka mana sai sunyi mita, mu sa'o'in su ne?
Mamie cikin ɓata rai tace "tou ae suma su Raliyan sun kai su riƙe wayan, ae da sai suma a saya musu".
"Babu wanda zai saya musu waya sai sun gama makarantan suma, kuma sai anga result ɗinsu yayi kyau irin nasu Ayshaa, yaran da SS 1 zasu shiga gaggawan me akeyi"? Yayah Umar daya ke shigowa parlon shi da yayah ishaq ya faɗa, ganin haka mamie bata sake tankawa ba, sai tsaki da taja ƙasa-ƙasa.
Gaishe da kowa sukayi sannan suka nemi wuri suka zauna, Yayah ishaq yana duban hafsy data ɗano baki sama kaman zatayi kuka yace, "jerry kada ki damu, nine nan zan saya muku haɗaɗɗe keda tom, amma da sharaɗin babu sim, don kada ki addabe ni da flashing," yana zolayanta ya faɗa, don babu hali taga wayan ummi sai tayi flashing ɗinshi ya ƙira, idan ummi tayi magana tace shine fa kawai ya ƙira, dama tun tana ƙarama Aunty Rakiya da Aunty Asma'u suke zolayanta haɗin gidan shi, gashi babu dama taga yana wasa da Raliya zata zunɓura baki gaba, kowa saidai yayi dariya don yadda ko mu mukayi wasa da shi sai tayi fushi.
Mamah tace tou Allah ya nuna mana lokacin ishaq, amma flashin kam zaka sha shi a wurin wannan ƴar fitinan.
Babu wuya wurin ubangiji yadda lokaci yake ta tafiya har abun tsoro, a haka admission ɗinmu ya fito, ATBU ta bamu gurbin karatu, ranan da mukaje registration sai da muka tuna jamila, Allah sarki jammy besty, tayi burin shiga ATBU amma Allah yayi achan zatayi karatunta.
Course ɗaya muka samu nida jamilah wato *BUSINESS ADMIN* ita kuma habiba *COMPUTER SCIENCE* dama ita da jammy shi suka zaɓa tun lokacin jamb ɗin mu, sai Allah yayi ita bada ita za'ayi ba, kuma zuwa wannan lokacin Yayah Aliyu ya samu number nah ta wurin jammy waya mukeyi har lokacin ban bashi daman zuwa gida ba, don gaskiya ni tsoro nakeji, a haka kuma habiba tayi wani saurayi yana da wurin sai da mota, tana kula shi amma banga alaman zuciyar ta na kanshi ba, sbd da na mata magana sai tace mun yana da rawan kai da yawan surutu, ita bata son mai irin ɗabi'an shi, dama irin Aliyu ne tou bata da damuwa.
Tana faɗan haka na dube ta nace, "sisto tou ko na haɗaku da Aliyun ne? Don ni kinga gaskiya bai mun ba, fari nake so",
Hmmm, "sisto kenan ina kika taɓa ganin anyi haka? Shima ae bazai yadda ba, tunda ae ya ganni amma bai ce ni yake so ba sai ke, kawai dai akwai lokaci sisto,yanzu ne fah muke cika 17yrs, me ma mukayi?" ta faɗa tana maida hankalinta kan wayanta, nidai tsura mata ido nayi ina kallon ta, chan na sake cewa "amma dai sisto idan an mana aure sumul zamu zauna, kuma har mu haihu, kinga ae jamilah har ciki fah take dashi, kuma gashi maryam ma ta samu saurayi ɗan abokin Baban ta, kuma ita ma muna shiga level 2 kinji aure zatayi, kawai na haɗaku nima sai na jira nawa rabon, kinga december this year auren Yayah Ahmed, mu kuma kawai irin next december sai a miƙa mu", na faɗa ina dariya, itama dariyan tayi tana "wayaga Aysha da habiba a ɗakin aure", gaba ɗaya muka kwashe da dariya, " sisto kin san me yake burgeni da aure"? Tana kallo na ta jijjiga kanta alaman a'a, na rausayar da kaina ina fari da ido nace, "na tashi da safe nayi breakfast wa miji na da ƴaƴana, shi zai tafi office su kuma school, ni kuma ina busy a kitchen", dariys muka sake kwashewa, habiba ta riƙo hannu na tace, "sisto ni kuma na ganni da ciki ina irin laulayin nan, nayi amai na dawo yana ta mun sorry wife, ni kuma ina ta shagwaɓa ina ni abu kaza zanci", dariya muka sake tun tsirewa da shi, cikin dariya nace, "Allah yasa muyi aure rana ɗaya sisto" Ameen mukaji hajiya ummah ta amsa, tana ƙara shigowa cikin ɗakin.
Zaro ido nayi ina kallonta cike da mamaki, wato tsohuwar nan laɓe ta fara mana ko mai?
"yakamata nayi zama da ɗana, domin na shaidah masa inda yaran da yake yabo suka dosa, don alama ya fara nuna kun ƙosa, kun ƙosa mana tunda har lissafin ciki ku ka fara, Allah ya nufa ma baku kai da lissafin kwanciya ba, kafin aje a haka gara ya samu labari" ta faɗa tana ɗirkawa habiba dundo a baya tana, "babu ma yake, domin na lura jaraba irin na uwarki duk kin haddace, sai dai Allah ya rufa asiri.
Tana cikin sababinta Yayah mohd ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, yana "kefa tsohuwar nan fitina ne da ke, mutum yana ta sallama ke kuma kina ta sababi ba bazaki saurara ba, kuma kizo kina cewa ba'a miki sallama ba,
Ina zan saurareka yai nakama yaran nan da ake musu kallon sallah -sallah amma ashe ko alwala basu iya ba, dama ina cike dasu yadda ɗana kullum bakin shi yabon shi akan sune, don koni da nayi namijin ƙoƙari wurin haihuwar shi baya gani ballantana kaji ya yabeni, sai waƴannan masu kai kaman na zabuwa",
Dariya yayah mohd yayi yana miƙo mana hannu yana faɗin , "kuzo muje parlor kumun bayanin yayah karatun ATBU yake"?
Hararan mu hajiya ummah tayi, tana ya mutsa fuska tace, "ae ni shirme ma nayi da na gaya maka me sukayi, don babu wani mataki da zaka iya ɗauka, dama Ummaru ne, na sanshi aiki ne da cikawa", mudai babu wanda ya kulata don sanin halinta yanzu zata zageka, idan wani kuma ya taɓa ka sai inda ƙarfin ta kuma ya ƙare.
A haka watan azumi ya shigo, kowa ka ganshi sai shirin shiga watan Ramadan akeyi, ko ina sai sayayyah ake, haka ƴan'uwa na Yayah mohd da yayah Ahmad suka haɗo kayan azumi wa Abba, don yanzu komai sun tsaya akai, basu wani jiran Abba yayi, yayah umar kuma suna shirin tafiya service, shi Kaduna a ka cillashi, yayah ishaq kuma Benin, haka suka shirya suka tafi, azumi nada kwana uku mummyn jamila tazo gidan mu, abin mamaki boot ɗin mutanta shaƙe da kayan Azumi, doya ne dankali ne fruit ne, wai duk toshi ta kawo, sai farin ciki kawai zaka gani a saman fuskanta, ummi da mamah ne suka karɓeta cikin mutunci, suna tambayanta labarin jamilah a chan inda ta ke, nidai bayan nagaishe ta guduwa side ɗin hjy ummah nayi, rai na duk a ɓace, bayan nagayawa Aliyu kada ya fara saka mama tazo, donni tsoro nakeji a sani a gida, amma nayi imani yau kowa sai ya sani, raina a ɓace haabiba ta isoni, kallo ne takeyi cike da damuwa tace, "Sisto tou meye laifin Aliyun nan ne? Nifa banga makusa fah a tare da shi, kawai ki amince, inaga auren farin mutum wani abu ne?" hararanta nayi nace mata ni bani da ra'ayi akan shi, kawai ya rabu dani, tana kallo na tace tou ki gaya mishi mana kafin komai yayi nisa.
Zuwa dare ummi ta ƙirani, tambaya na tayi game da alaƙan dake tsakanin mu da Aliyu wanda ban taɓa gaya mata ba, rai na a jagule na dubeta nace, " ummi nifa bana son shi, nace mishi ma fah ya nemi habiba saboda ita ya mata, amma shine yakama ya gayawa mummy, nidai ummi bana son shi".
Kallo kawai ta bini da shi, sannan tace, "a wani gari kika taɓa ganin anyi haka? Ina ke yagani yake so? Meya kawo maganan habiba kuma, ko yace miki yama sonta ne?"
"Nidai kawai ummi bana son shi, ita kuma ya mata gara kawai ya nemeta," "Allah ya kyauta, Allah ya muku zaɓi na alkhairi inji ummi.
Ganin yadda nayi ummi sai ta ɓoye bata gayawa Abba zuwan mummy ba, kuma ta kwaɓi mamah mah,
A haka satin sallah ya shigo, gaba ɗayan mu ranan mun karɓo ɗin kunan mu, sai murna muketayi gaskiya *JAMILAH HANCO* ta chanchara mana ɗinkuna masu kyau , da safe bayan mun dawo daga tafseer sai ga driver gidan su jamilah ya kawo kaya kusan kala biyar a ɗinke, da wani abayah mai masifan kyau da tsadan gaske, ɗaya ledan kuma jaka ne da kalmi set 2, haka mummy ta haɗo aka kawo wai duk kayan sallah nane, ummi ta ƙirah mama akan suyi shawarah, haka mamah ta bata shawaran kawai ta sanar da Abba kada abu yayi nisa, nidai ko kaɗan kayan basu mun ba, don bana son mai kayan ballantana kayan, kawai kunyar jamilah ne yasa nake raga mishi, amma sai ya ƙirani sama da goma ban ɗauki wayan shi sau biyu ba, yawanci habiba ce ma ke ɗauka suyita hira akan course ɗinta, nidai nawa ido, a haka yace mun ran sallah zai turo a nema mishi ison zuwa muna gaisawa nidai ƙin amince mishi nayi sai habiba ne tace mishi babu damuwa hakan ma yayi.
*AUNTY NICE*
managarciya