Tsaro: Lakurawa sun kashe 'yan sanda uku a Kebbi

Tsaro: Lakurawa sun kashe 'yan sanda uku a Kebbi

'Yan bindiga da ake zargin Lukurawa ne a ranar Juma'a sun kai farmaki a garin Zogirma-Tilli dake kan haryar karamar hukumar Bunza a jihar Kebbi a lokacin da suka yi yunkurin garkuwa da wasu direbobin mota dake bin hanyar.

A bayanin da 'yan sanda suka samu ne ya sa suka taso a tawaga domin kawo dauki ga jama'a a cikin motar su ta sintiri suka zo wurin, sun yi ta musayar wuta da 'yan bindigar abin da ya kai ga kashe dan sanda uku ciki har da mai mukamin Insifekta.

Bayanin na kunshe ne a cikin rahoton da maimagana da yawun 'yan sandan Kebbi Nafi'u Abubakar ya fitar, da yawan 'yan bindigar an tura su barzahu a musayar wutar.
Kwamishinan 'yan sanda Bello Sani ya jinjina kan sadaukarwa da zaƙaƙuran 'yan sandan suka yi don kare mutanen ƙasa.
Haka kuma rundunar sojoji bataliya 223 dake ƙaramar hukumar Zuru sun kare wani hari da 'yan bindigar suka kawo a garin Riɓah na ƙaramar hukumar Danko Wasagu duk a jihar Kebbi.

Sun yi nasarar hana sama da 'yan bindiga 400 kokarin shiga garin don su tayar da shi, ɓarin wutar ya sa 'yan bindigar suka koma bayan yi masu rauni da jikata su.

Daraktan tsaro na jihar Alhaji Abdulrahman Zagga ya jijinawa sojojin kan sadaukarwar su.
"Harin 'yan bindigar ya gaza samun nasara ne saboda ƙwarewa da gogewar sojojinmu a dole suka ja baya don sun haɗu da mayaƙa na gaskiya."