ƘADDARA TA: Fita Ta 15

"Innalillahi wa inna ilaihiraji'un" sai a sannan ya samu wani irin kuka yazo mishi, tsohon ne ya shigo gidan ya ganshi yana kuka, jikinshi a sanyaye ya zauna yana tambaya meya sameshi? tsohuwar ce ta bashi labari kaf babu ɓata ko ɗaya a cikin maganan, shiru yayi yana kallon najeeb dake kuka kamar zai mutu, kwanciya yayi a kasa yana kuka me taɓa zuciya, a hankali yace

ƘADDARA TA: Fita Ta 15


 ƘADDARA TA: 


        Na
*Jiddah S Mapi*


*Chapter 15*


                  ~Shiga ciki yayi jin basu amsa ba, ya kalli cikin gidan da komai yake a rufe harda kofanshi da kofansu, cikin ruwan da jikinshi yake yi ya buɗe kofan, gani yayi babu komai ya fita ya buɗe nashi wayam babu komai, jiri duhu duk suka kamashi a lokaci ɗaya, a tsakar gida ya zauna ya rike kanshi da yake sarawa yace "Asmeeta? Asmee? mimi? Ameena? kar kumin haka ina kuke?"
sallaman da yaji yasa ya juyo makociyarsu ce wata kinibabbiyar tsohuwa tace "najeebu kaine kayi kuɗi haka? najeebu ko dai kuɗi kayi dasu Asmee? sabida tunda ka tafi mimi ta kwanta rashin lafiya wannan fitsararriyar kanwar taka taje wajen me shayi ta damfareshi kuɗaɗe masu yawa suka bar garin ba tareda kowa ya sani ba har yau babu labarinsu.
dafa kai yayi yace "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un"
sai a sannan ya samu wani irin kuka yazo mishi, tsohon ne ya shigo gidan ya ganshi yana kuka, jikinshi a sanyaye ya zauna yana tambaya meya sameshi?
tsohuwar ce ta bashi labari kaf babu ɓata ko ɗaya a cikin maganan, shiru yayi yana kallon najeeb dake kuka kamar zai mutu, kwanciya yayi a kasa yana kuka me taɓa zuciya, a hankali yace "kayi hakuri kowane ɗan adam da irin kaddaran da Allah ya tsara mishi kuma babu yadda zaka tsallake, wani sai yayi kuɗi yake fuskantan jarabawa wani kuma da talauci yake fuskanta duk abinda ya faru kayi addu'a Allah yasa hakan shine daidai"
yace "wallahi na yafe duk kuɗin da nayi na yafe a dawomin dasu na yadda mu zauna cikin talaucin da muke banason kuɗin"
cikin lallashi yace "hakan kamar kana faɗawa Allah ne kuɗin daya baka bai kamata ba da addu'a kayi da yafi akan maganan da kake yi"
duk yadda sukayi dashi ya tashi yaki tashi a wajen ya wuni yana kuka yana dana sanin tafiya da yayi ya barsu, yana ɗaurawa kanshi alhakin komai.
wasa wasa a wajen ya kwana kwance a kasa yana tuna amanan Asmeeta da iyayensu suka bashi, shine ya rasa asmeeta da duk duniya babu abinda yake so kamar ita, hasalima kullum addu'an da yake yi na samun kuɗi sabida ita yake yi gashi yau ya samu kuɗin amma ya rasata.
yayi kwana uku a gidan yaki tafiya baba ne yake kula dashi domin har rashin lafiya yayi, kaka tana kawo musu abinci daya kalli ɗakinsu sai kuka, kullum cikin nasiha baba yake mishi, da kyar ya fara cin abinci, saida sukayi sati yana ganin kamar zasu dawo ya tabbatar ba zasu dawo ba ya tashi cikin kasala yacewa baba zasu tafi yau, shiru baba yayi yana kallonshi yace "zaka tafi kenan ka barni?"
ya girgiza kai yace "zamu tafi tare"
fuskanshi kamar bashi ba, ya rikiɗe ya koma asalin najeeb wanda ya taso cikin wahala baya dariya baya walwala da mutane, ya zama kamar be taɓa dariya ba, dama Asmeeta da mimi kaɗai yake kallo yayi dariya yau babu su dariyanshi ya kare a rayuwarshi yana ji ba zai sake dariya ba shikenan rayuwa ya tafi da duk wani walwala da farin cikinshi, har suka shiga mota kaka ta fara kuka sabida ta san da wuya ya kara dawowa, kuɗi me yawa ya bata sannan ya ɗauke kai yana hawaye yaja motan ya tafi, kuka yake yi sosai yana driving har yayi nisa da kauyen bai daina kuka ba, baba ma hawayen yake domin duk wanda yaga najeeb kuma yasan rayuwarshi saiya mishi kuka, gidanshi me bala'in kyau da tsada ya tsaya da motan yayi hon, fadeel wanda yake cikin damuwa shima abin duniyan ya isheshi sabida rashin dawowan najeeb wanda suka saba sosai ya ɗaukeshi tamkar yayanshi wanda suka fito ciki ɗaya, yana zaune a garden na gidan yayi tagumi yana jin sanyi yaji hon, da sauri ya tashi yaje ya buɗe kofan ya leka domin a tsorace yake, sauke glass najeeb yayi yana ganinshi ya kasa buɗe gate ɗin fita yayi da gudu ganin haka najeeb ya buɗe marfin motan ya fito, wani irin rungumeshi yayi ya fara kuka, shima najeeb kuka ya fara yana tuna komai daya faru, baba dake cikin mota jikinshi ya kara sanyi, da kyar najeeb ya lallashi kanshi sannan ya fara bubbuga bayanshi a hankali alaman yayi shiru, shiru yayi ya ɗan zame jikinshi yace "nayi tsammanin ba zaka dawo ba harna fara tunanin tafiya nima kullum cikin tsoro nake yaya gidan yamin girma"
a hankali ya share mishi hawayen yace "ba gashi na dawo ba?"
ya leka motan yace "ina matarka? ina kanwarka? ina kuma ƴar kanwarka ɗin?"
girgiza kai yayi ya ɗauke kai hawaye yana wanke mishi fuska, yace "babu su"
da mamaki yace "babu su kuma?"
juyowa yayi yana kallon fadeel da kyawawan idanunshi irin na turawa yace "naje sun ɓata basa garin ance sun jirani sun jirani har sun gaji sun tafi"
kuka ya fashe dashi, a hankali fadeel ya rungumeshi saida ya barshi yayi kuka me isanshi kafin yace "sorry yaya insha Allah ba zasu ɓata ba watarana zakuga juna"
yace "fadeel ban taɓa jin ka tsani arziki ba saida na koma gida naga babu kowa nawa, babu wacce nakejin zan iya rayuwa da talauci har karshen rayuwata akanta sai kanwata da mahaifiyarmu ta mutu tana cewa ta barmin ita amana, babu amfanin dukiya a wajena duk banza nake kallonsu"
shiru fadeel yayi shima maraya ne yasan zafin maraici duk da zaman da yayi a gidan yayan babanshi sarki bai fuskanshi wani kiyayya daga garesu ba amma daga karshe yaji ya tsanesu tunda suka barshi rayuwarshi taso ta ɓaci yaso ya fara bin masu shaye shaye ya fara sata yaji babu waɗanda yake gaba dasu a halin yanzu kamar duk ƴan gidan sarkin, da zai samu dama da saiya kona gidan gaba ɗaya kowa ya mutu, musamman da zai tafi da waziri yace mishi ana zargin sarki ne ya kashe iyayenshi sabida hameed ya zama sarki idan sarki ya mutu hakan yasa yaji ya kullaci ƴan gidan sarki ya tsani sarki da hameed wanda shine zai zamo sarki idan babu Abi, a halin yanzu najeeb ne kaɗai ɗan uwanshi bayan shi yasa a ranshi duk ƴan uwanshi sun mutu harda sultan wanda tsanan mahaifinshi ya shafeshi"
rike najeeb yayi cikin son da yake mishi na taimakon rayuwarshi suka shiga gida da mamaki yaga baba dake cikin matan yaja motan ya shigo dashi, najeeb cikin rashin fara'anshi ya faɗa mishi yadda ya haɗu da baba, zasu shiga ciki yace ya buɗe bayan motan akwai dutsen gold daya zo dashi, cikin respect yace "to yaya"
buɗe motan yayi ya ɗauko sannan yabi bayansu ya shigo, zama a zazzafan farin sofan dake ɗakin najeeb yayi sannan ya dafa kanshi yana kallon makeken tv dake manne a jikin bango, fadeel ne ya shiga kitchen ya fara musu girki duk da bai iya ba amma yayi kokari yasa a plate ya kawowa kowa sannan shima ya zauna ya fara ci, najeeb kaɗan yaci yasha ruwa yace "zan shiga ciki ka nunawa baba wancan ɗayan ɗakin a ciki zai zauna kai kuma tare zamu zauna duk da akwai ɗakuna nafi son mu zauna tare domin yanzu kai kaɗai nake dashi sai baba"
yace "to yaya insha Allah"
shiga ciki yayi ya kwanta akan gadon yayi shiru, ameena wacce ya tafi ya bari bayan ya lashi zuman da ba zai taɓa mantawa ba yaji yana tausayin kanshi a duk inda take yasan yanzu tana dakon soyayyanshi, yasan zata kula mishi da mimi da Asmeeta, share hawaye yayi yace "ki kulamin da kanwata dan Allah kada ki karya alkawari".

Cikin kuka Asmee tace "wacece ita a wannan gidan?"
tace "matar hameed ce"
tana kuka tace "to me nayi mata ta tsaneni? meyasa kullum take tsangwamata? me haɗina da ita?"
salma cikin lallashi tace "kiyi hakuri Asmee ki barta da halinta"
share hawaye tayi tace "shikenan ba komai"
tace "amma ƴar sarkin wani gari ne?"
tace "ba ƴar sarki bace accident sukayi iyayenta suka rasu shine ya kaseem babban ɗan sarki ya ɗaukota ya kawota gidan daga nan suka yaba da halinta suka aurawa yarima hameed"
tace "ba ƴar sarki ba kuma? taya haka ya kasance? to ya akayi tace min bayin gidansu ma ta tsanesu? kuma ai yanayinta da yadda take yin abu baiyi kama dana marainiya ba"
tace "iyayenta duk sun mutu kuma talakawa ne"
girgiza kai asmee tayi tace "wannan ƴar sarki ce domin tayi suɓutan baki ta faɗamin da bakinta"
salma tace "Asmee ki iya bakinki asmee kada kisa ido akan abinda be shafeki ba"
tace "salma baki sanni ba tunda na taso a kauyenmu nake gaba da ƴammatan da suka ɗau karan tsana suka ɗaura min sannan duk wacce ta nemeni da gaba wallahi bana barinta sai na sata a gaba itama tunda ta nema kuma ta siyi faɗana da kuɗinta wallahi saina rama, ba matar kurman ɗan sarki ba ko matar sarkin ne da kanta saina rama bale ita, kuma na fara zargin karya tayi musu sabida ta auri yarima"
salma tace "A,a Asmee ina rabaki, ina rabaki asmee"
tsaki taja taje taci gaba da wankin kayan da Aneetan ta bata wanda tun safe take yi har yanzu, da kyar ta gama ta zauna a karkashin bishiya tana kallon mutanen dake shige da fice a gidan, uniform ɗin bayin ya karɓeta sosai fuskanta kamar na balarabiya, kaseem ne ya fito cikin sauri yana waya yace "gani nan zuwa yanzu ba zan jima ba"
motarshi ya shiga da sauri ya tada, Asmee dake zaune ta kalli gaban motan sai taga kamar ruwa ne yake ɗiga daga cikin motan, gani tayi motan yana hayaki da gudu ta tashi taje ta fara knocking glass ɗin, kallonta yayi da mamakin meyasa take knocking?
sauke glass ɗin yayi zuwa lokacin wajen yayi zafi harma ya fara hayakin sosai gab yake da kamawa da wuta, gani tayi wani daga cikin masu aikin gidan yazo kamar ba'a ganinshi ya kunna ashana ya wurga, da karfi taja hanun ya kaseem da yake kallonta, fitowa yayi a motan, tureshi tayi suka faɗi a gefe, take motan ya kama da wuta, kallonta yake tana rike dashi manyan idanunta suna waje tsaban tsoro, shima a tsorace yake kallon motan da yake ci da wuta, manyan idanunta ta sauke akan me aikin da yake shirin gudu, ture ya kaseem tayi tace "gashi can shine yasa wutan"
ganin tana nunashi ya fara gudu, binshi ta fara masu gadi sunzo wajen da wuta yake ci sun manta da kofa a buɗe, fita yayi da gudun ceton rai Asmeeta binshi ta fara kira halin kaka kuma saita kamashi domin tanada kafiya, kaseem tashi yayi ganin ta bishi kar yaje ya mata illa shima kawai ya bisu,
gudu yayi gudu ya wurgar da takalminshi Asmee bata karaya ba binshi take itama dama tun a kauye ta iya gudu domin idan taje satan mangoro babu me iya kamata, tuntuɓe yayi da dutse ya faɗi ƙasa zai tashi ta cafke bayan riganshi, mayar dashi kasa tayi ta fara kai mishi duka cikin karfin hali tace "waya saka kisa? waya saka?"
yace "dan Allah...."
duka ta kara kai mishi tace "waya saka ka ƙona mutum da ranshi?"
ta shaƙe wuyanshi ta yadda zaiji zafi ya faɗa
a wahale yace "A...."
karan harbi taji sai kuma taga goshinshi yana jini duba bayanshi tayi taga an harbeshi, a razane ta kalli bayanshi bataga kowa ba, kaseem da yaga time ɗin da akayi harbin ya kasa karasowa ganin ya mutu a hanun Asmee.
dafa kai yayi yace "Innalillahi"
Asmee jikinta ya fara rawa da sauri ta sakeshi ta tashi, kaseem da kyar ya karaso yana haƙi yace "ya faɗa miki wanda ya sashi?"
girgiza kai tayi tace "ya...ya...ya fara magana sai yayi shiru"
yace "me ya fara faɗa?"
tace "da nace waya sashi kona mutum da ranshi shine yace A... daga nan aka harbeshi ya mutu"
tayi maganan cikin firgici domin bata taɓa ganin mutum ya mutu a gabanta ba, yace "kar kiji tsoro babu abinda zai sameki na gode na gode na gode"
shiru tayi, yace "muje"
tace "to yaya zamuyi dashi?"
yace "karki damu za'a zo a ɗaukeshi anan"
tafiya sukayi har yanzu jikinta yana rawa, gidan suka koma kowa ya fara mishi sannu, shiru yayi kawai ya shiga ciki, duk suna falo kowa yana cikin ruɗani harda Aneeta dake sanye da bakin kaya, hanun Asmee ya rike yace "muje"
tace "ina kuma zanje?"
baiyi magana ba ya shiga ciki da ita, suna ganinshi suka tashi kowa yana tambayan babu abinda ya sameshi?
a tsakiya ya tsayar da Asmeeta yace "wannan itace ta ceci rayuwata da yaddan Allah yau, inaso ki maimaita abinda ya faɗa a lokacin da kika tambayeshi waya sashi?"
tana rarraba manyan idanunta tace "ya ambaci kalman A sai aka harbeshi"
cikin zafin zuciya kaseem yace "a gidannan kenan wani yasa a kasheni? a konani da raina?"
Ammi tace "to kaseem wa kake zargin zaisa a kona ka?"
murmushin takaici yayi yace "Ammi kece kikasa?"
da sauri tace "ni kuma kaseem bani bace"
yazo gaban Aneeta yace "Aneeta kece kika sa?"
ta girgiza kai tace "bani bace"
ya kalli hameed yace "Abdulhameed kaine?"
cikin son yayanshi ya girgiza kai, yazo gaban meenat yace "Ameenat kece?"
kallonta asmee tayi jin sunan daya kirata dashi, Ameenat kenan sunan ameena da suke kiranta dashi basuyi kuskure ba, tace "yaya me zaisa na kasheka?"
ya kalli Abi yace "Abi ko kaine?"
girgiza kai yayi, yace "Alameen kana gidannan yau ko kaine?"
yayi saurin girgiza kai, yace "to shikenan kowa yace bashi bane"
Ammi tace "kaima ya kamata ka tambayi kanka watakila kaine kasa ayi maka hakan ko ka manta kaima Alkaseem ne?"
ya girgiza kai yace "bani bane"
kallo stair yayi yace "ina zuwa"
ɗakinshi ya shiga ya dawo har yanzu suna tsaye a inda ya barsu, hanyan fita ya nufa Aneeta tace "itama ka manta baka tambayeta ba sabida itama ai Asmeeta ce A ne farin sunanta"
yace "tayaya wacce ta ceceni zata kasheni? me haɗinta dani?"
Ammi tace "to yanzu wa kake zargi?"
yace "mutum ɗaya ne tunda duk kunce baku bane mutum ɗaya ne kawai zai iya kuma kafin ya kasheni ni zan kashe shi"
yayi magana yana nuna musu bindigan hanunshi yasa hanu a handle zai fita, rikeshi hameed yayi yace "hameed sakeni"
Asmeeta ganin bindiga taji hantar cikinta ya kaɗa jikinta ya fara rawa, wani kallo da Aneeta take binta dashi shi yake kara tsurar da ita, gani tayi hameed ya durkusa kasa ya haɗa hanu biyu yana hawaye, kallonshi asmee takeyi yadda yake hawaye yafi komai tsaya mata a rai, cikin sanyin jiki kaseem ya durkusa ya haɗa hanunshi da nashi daya haɗa ya rungumeshi, a hankali ya zameshi yana share mishi hawayen cikin sanyin murya yace "na fasa yarima kar kayi kuka"
jikin Asmeeta bai taɓa sanyi ba irin na yau, tana ganinshi da girman kai da rashin kula mutane amma da taga hawaye a idonshi sai taji ya bata tausayi, tana ganin magana a bakinshi amma baida hanyan furtawa, a hankali taja jikinta ta fita, ɗakinsu taje ta zauna akan katifan tayi shiru, lumshe ido tayi, taga yadda yake haɗa hanu yana kuka a durkushe bayan hamma najeeb babu wanda ta kara jin tausayinshi a duniya kamar hameed, salma wacce ta gaji tazo ta aje mata abinci tace "gashi kici"
girgiza kai tayi tace "zauna mana salma"
zama tayi, tace "an taɓa nemawa yarima maganin wannan rashin maganan da yake?"
tace "eh to kamar naji ance sun taɓa nema mishi magani amma bai dace ba daga nan basu kara nema ba dan wai ance ba zai taɓa warkewa ba"
tace "zai warke mana salma ai babu cutan da babu magani a duniya"
salma tace "to saide addu'a"
tayi shiru kawai data rufe ido fa ganinshi take.

_Jiddah Ce..._
 08144818849