Ɗariƙar Tijjaniya Ta Yi Rashin Wani Babban Malami A Nijeriya
Duniyar musulunci tayi babban rashi Allah ya yiwa sarkin malaman Zuru Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe rasuwa.
Allah ya karbi rayuwar Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe Zuru babban malamin Tijjaniyya,
Allah ya yiwa babban malamin musulunci kuma shehun Darikar Tijjaniyya a Najeriya Sheikh Abdulrahman Hamza Balarabe Zuru da ke Jihar Kebbi a arewacin Najeriya, rasuwa.
Shehin malamin ya bada gagarumar gudunmuwa a addinin islama Najeriya ya kasance mutum mai tawali'u da tsaron Allah tausayi da kuma taimakon addinin Allah.
Allah ya jikansa da rahama ya kyautata tamu bayan tasu alfarmar Al'qur'an.
Daga Abbakar Aleeyu Anache
managarciya