Rikicin  PDP Ya Fito Fili, Gwamnoni 8 Sun Kauracewa  Taron Jam’iyya

Rikicin  PDP Ya Fito Fili, Gwamnoni 8 Sun Kauracewa  Taron Jam’iyya


Akalla gwamnonin jihohi takwas ne ba a gani ba a wajen wani taro na jam’iyyar PDP da aka shirya a ranar Laraba, 7 ga watan Satumba 2022. Labarin da muka samu daga gidan talabijin na AIT shi ne shugabannin jam’iyyar hamayyar sun yi zama ne a Abuja, inda aka tattauna batutuwan zabe.

Taron ya samu halartar shugaban jam’iyya na kasa, Iyorchia Ayu da shugaban majalisar amintattu, Walid Jibrin, wanda ake zargin kujerunsu na rawa. 
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Arch. Muhammad Namadi Sambo da Atiku Abubakar sun je wajen taron, amma ba a ga keyar wasu gwamnoni ba. 
Rahoton yace an shirya taron ne da nufin magance rigimar cikin gidan da ta bijiro bayan tsaida ‘dan takara, sai dai da alama, ba a kai ga yin sulhu ba. 
Nyesom Wike da gwamnonin jihohin PDP da ke tare da shi wajen rigima da bangaren Atiku Abubakar, sun yi amfani da taron wajen fito da fushin na su. 
Aminu Waziri Tambuwal shi ne shugaban kungiyar gwamnonin jihohin da PDP ta ke mulki. 
Gwamnan na Sokoto yana cikin na gaban goshin ‘dan takaran. Bayan taron, Sakataren yada labaran PDP na kasa, Debo Ologunagba yace har aka tashi wannan zama, ba ayi maganar shugaban PDP ya yi murabus ba.