Magidanci Ya Roki Kotu Ta Raba Aurensa Kar Matar Ta Kashe Shi
Wani magidanci kuma ma’aikacin gwamnati a Babban Birnin Tarayya Abuja mai suna Aku Bakare ya garzaya kotu a Nyanya inda ya roki kotun ta raba auren sa da matarsa Mary saboda yadda take yi masa barazanar za ta kashe shi.
Bakare dake zama a Nyanya ya ce ya fada wa matarsa Mary ta tattara kayan ta ta fice masa daga gida ta koma cocin da suke zuwa shekaru 15 da suka gabata bayan ta yi kokarin kashesa lokuta da dama.
“Da ni da gidana amma kullum ina cikin fargaba da tsoro.
“Mary bata kula da ni kamar yadda mace ya kamata ta rika kula da mijinta.
Bakare ya ce akwai ranar da ta dauko sharbebiyar wuka ta nufo i gadan-gadan don ta kashe ni, Allah ya bai sa’a na murkushe ta da karfin tsiya na kwace wukar da tuni in barzahu.
“Haka kuma ta taba mamaya ta ta cafke min ‘ya’yan marainai na ta nemi ta murje su, Allah ya taimake ni ‘ya’yan mu na nan suka kawo min dauki, shima da tuni na sheka lahira.
“ A kullum ba ta gidanta idan ka tambaye ta in ta ke sai ta ce tana coci, bata damu da ni mujinta ba, ballanta gidanta ma.
Alkalin kotun Doocivir Yawe ta yi kira ga ma’auratan da su je gidan su sassanta kansu.
Doocivir ta ce za a cigaba da shari’a ranar 16 ga Janairu.
managarciya