Ɗan majalisar wakilai a Kebbi ya kaddamar da ba da tallafin kudin karatu da Laptop  ga dalibai 200

Ɗan majalisar wakilai a Kebbi ya kaddamar da ba da tallafin kudin karatu da Laptop  ga dalibai 200

Dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Zuru Fakai Danko Wasagu Sakaba da ke jihar Kebbi Hon Kabir Tukura ya kaddamar da rabon kudin karatu da laptop ga dalibai 200:

Honourable Kabir Tukura ya kaddamar da wannan tallafin ne ga daliban manyan makarantu daban daban yan asalin Zuru Fakai Danko Wasagu Sakaba.

Tukura ya bada tabbacin cewa zai ci gaba da kyautata jin dadi da walwalar dalibai a kowane mataki domin inganta rayuwarsu.

Sannan kuma Hon Kabir Ibrahim Tukura ya bada tallafin Nairi dubu dari ga kowane dalibi mutum 200: da laptop laptop domin inganta harkokin ilimi.

Shuwagabannin jam'iyyar APC Zuru Fakai Danko Wasagu Sakaba sun yi godiya tare da jinjinawa Gamjin Zuru bisa kokarinsa na baiwa ilimi fifiko da kuma samar da ayyukan raya kasa.

Taron ya samu halartar manyan baki ciki hadda mataimakin shugaban karamar hukumar Zuru Hon Samaila Abdullahi.

Gamjin Zuru ya yi jinjina tare da  yaba wa gwamnan kebbi Dr, Nasir Idris Garkuwan Zuru wajen namijin kokarinsa ga al'ummar jihar Kebbi.

Daga Abbakar Aleeyu Anache