Za a ci gaba da bai wa jihar Rivers kason ta na wata-wata - Ofishin Akanta Janar

Za a ci gaba da bai wa jihar Rivers kason ta na wata-wata - Ofishin Akanta Janar

Ofishin Akanta-Janar na Tarayya  ya ce Jihar Ribas za ta karɓi kuɗin rabon tallafin kuɗaɗe daga gwamnatin tarayya bayan daukaka kara da gwamnatin jihar ta yi.

Bawa Mokwa, daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a na ofishin, ya bayyana haka ga jaridar TheCable a ranar Asabar.

Ya ce, ko da yake akwai umarnin kotu da ya hana rabon kuɗaɗen ga jihar, hukuncin kotun daukaka kara ya fi ƙarfin umarnin kotun farko.

"Za mu bi umarnin kotu. Jiya, bayan wani rahoto da ya ce ba za a biya Jihar Ribas ba, gwamnatin jihar ta aika da sanarwar daukaka kara kan batun," in ji shi.

"Don haka, a bayyane yake za mu bi umarnin kotu. Wannan sanarwa ta nuna cewa an dakatar da aiwatar da hukuncin farko, wanda ke nufin za mu ci gaba da abin da aka saba. Wannan yana nufin jihar za ta samu rabonta na kuɗaɗen tallafi."