Rikicin APC:Buni Ya Karyata El-Rufa'i Kan Buhari Ya Cire Shi

Rikicin APC:Buni Ya Karyata El-Rufa'i Kan Buhari Ya Cire Shi

 

Rikicin da jam'iyar APC ke fama da shi ya ci gaba, gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ya fitar da wata wasika da yake karyata gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i kan cewa an cire shi daga shugabancin jam'iyar APC na rikon kwarya wanda zai shirya babban taron kasa na jam'iyar.

Wasikar ta musanta maganar Nasir cewa an cire Buni daga shugabancin jam'iyya.
Bangaren Buni sun ce kafin ya yi tafiya a hukumance ya mika ragamar jagorancin jam'iya a hannun gwamnan Neja Abubakar Sani Bello.
Magoya bayan sun ce a takaradar Mai Mala ya rubuta a 28 ga watan Fabarairu ya umarci Abubakar Sani ya ci gaba jan ragamar jam'iyar domin zai je Dubai wajen duba lafiyarssa. Takardar an kaiwa hukumar zabe tun a lokacin.
Daya daga cikin jami'an Buni ya ce Mai Mala ba wanda ya cire shi ko wata kungiyar gwamnoni saboda ya bi doka ya nada Sani Bello ya zama mukaddashinsa kafin ya tafi.

Ya kalubalanci El-rufa'i ya sanar da mutanen Nijeriya abin da ya wakana tsakanin gwamnoni da Buhari a ranar lahadi da suka ziyarci fadar shugaban kasa.

Ya ce mutanen Nijeriya su tambayi Abubakar da mambobin kwamiti in takardar Buni ba ta same su ba.