Wasu Ɓatagari Sun Daddatse Wata Mata Har Lahira A Kano

Wasu Ɓatagari Sun Daddatse Wata Mata Har Lahira A Kano

Al'ummar garin Guringawa da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso a Jihar Kano sun tashi cikin wani gagarumin tashin hankali bayan da a ka tsinci gawar mace an daddatsa ta an jefar da ita a wani kango.

Mutanen garin sun baiyana cewa yara ne su ka gano gawar bayan da su ke wasan ɓuya, bayan da su ka ga jini yana kwaranyowa daga cikin kangon, lamarin da ya sanya su ka garzaya don su ga menene.

Mutanen sun ƙara da cewa bayan da yaran su ka shiga kangon ne sai su ka ga ashe jinin da ga cikin wani buhu ga ke kwararo wa, inda a firgice, su ka tafi su ka gayawa manya a wajen.

Bayan da manya su ka zo ne, har da mai-unguwar yankin, Alhaji Ghali Sulaiman sai su ka ga cewa ashe jikin mace ne an daddatsa shi, lamarin da ya sanya a ka ƙasa gane ko wacece.

Wata mata a garin, wacce ta nemi a sakaya sunanta ta baiyana cewa an ɗan samun irin wannan matsalar a yankin, inda ta ce ba wannan ba ne karon farko da a ke samun irin wannan aika-aikar a garin.

Ta kuma kara da cewa shi wannan kangon ya zama matattarar ɓatagari da kuma jibge shara.

A nashi ɓangaren, Mai-unguwa Sulaiman ya yi kira ga al'ummar garin da su yi hakuri su kwantar da hankali, inda ya ƙara da cewa an sanar da hukumomin da su ka dace.

Kakakin Rundunar Ƴan Sanda ta Kano, Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da faruwar al'amarin, inda ya baiyana cewa tuni jami'an bincike na rundunar su ka fara aiki da kuma faɗaɗa bincike har sai an kamo ɓata-garin da su ka aikata wannan ta'asa.