Sulhu A Neja: Ɗan Takarar Kujerar Gwamnan  A APC Ya Ziyarci Majalisar Zartarwa Ta Jiha

Sulhu A Neja: Ɗan Takarar Kujerar Gwamnan  A APC Ya Ziyarci Majalisar Zartarwa Ta Jiha
Daga Awwal Umar Kontagora, a Minna.
Dan takarar kujerar gwamnan Neja a jam'iyyar APC, Hon. Umar Muhammad Bago ya ziyarci majalisar zartaswa ta jiha dan yin sulhu ga gwamnatin jiha da wasu masu korafi a majalisar tare da gabatar da mataimakinsa, Kwamred Yakubu Garba.
Dan takarar wanda a yanzu shi ke wakiltar karamar hukumar Chanchaga a majalisar wakilai ta tarayya wanda yake zango na uku a majalisar, ya samu nasarar zama dan takarar ne bayan samun rinjaye ga sauran yan takarkarun da suke zama wannan matsayin.
Tunda farko tawagar ASB Group, Abubakar Sani Bello group da suka tallata gwamna mai ci Alhaji Abubakar Sani Bello a shekarar 2015 sun nemi gwamnan da ya nemi dan takarar da.ya baiwa kungiyar damar zakulo mataimaki a cikin su.
Rahotanni dai sun nuna cewar gwamnan bai amince da kudurin na su ba, domin bai marawa kowani dan takara baya ba, amma ya tabbatarwa kungiyar idan dan takarar ya nemi shi da wannan damar zai tabbatar mataimakin dan takarar zai fito ne a cikin su.
Bincike dai ya tabbatar da cewar kabilun gwarawa sun nuna rashin amincewarsu ga duk dan takarar da bai fitar da mataimaki a cikin su ba, domin jihar na bin tsarin karba karba ne.
A cewar kungiyar dattijan gwarawan sun ce tunda bangaren Neja ta kudu ne ta bada dan takara dole mataimaki ya fito a yankin su kuma ya zama cikakken bagware.
Dattijan sun mikawa dan takarar na APC sunayen mutane uku da suke son a fitar da mataimaki a cikin su, sunayen sune Dakta Mustapha Alheri tsohon kwamishinan masana'antu kuma wanda ya nemi takarar majalisar wakilai bai samu nasara ba, sai Dakta Usman Ahmed tsohon dan takarar kujerar gwamna da bai samu nasara ba, Injiniya Umar Ndanusa, na ukun shi ne shugaban kungiyar kwadago na jiha, Kwamared Yakubu Garba, wanda kuma shi ne ya samu nasarar zama mataimakin dan takarar bayan wani zaman masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC a jiha.
Hon. Bago, yace kowa yayi hakuri domin gwamnati tunbin giwa ce idan Allah ya bada nasarar da ake nema ba wanda gwamnati za ta bari a baya.