Tsarin mulkin Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala — ADC

Tsarin mulkin Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin wahala — ADC

Mai magana da yawun jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Bolaji Abdullahi, ya ce manufofin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa sun gaza rage radadin da ’yan Najeriya ke fuskanta.

A yayin wata tattaunawa a tashar Channels a ranar Laraba, Abdullahi ya caccaki salon tafiyar da tattalin arzikin kasar, yana mai cewa fa’idodin da aka yi alkawari ga talakawa har yanzu ba su bayyana ba.

“Manufofin wannan gwamnati ba suyi aiki ba,” in ji Abdullahi, yana mai cewa: “Mutane na cikin wahala, amma jami’an gwamnati suna tafiya da gagarumin ayari, suna rayuwa cikin alatu, yayin da kuke cewa talakawa su ci gaba da hakuri.”

Ya bayyana cewa akwai babbar gibin da ke tsakanin kalaman gwamnati da hakikanin rayuwar talaka.

Abdullahi ya kalubalanci gwamnati kan rashin fayyace wa’adin wahalar da ake sa ran mutane za su sha da kuma irin lada ko sauki da za su samu daga bisani.