Rikicin PDP: Shugabanni 4 Sun Mayar Da Kudi Miliyan 122  Da Aka Basu

Rikicin PDP: Shugabanni 4 Sun Mayar Da Kudi Miliyan 122  Da Aka Basu

Akalla mambobin kwamitin gudanarwa a  jam'iyyar adawa ta  PDP hudu sun mayar da kudi N122.4 million baitul malin jam'iyyar.

A wasikun da suka aikewa jam'iyar, mambobin sun bayyana cewa an tura wadannan kudade asusun bankunansu ne ba tare da izini ko sanninsu ba, rahoton ChannelsTV. 

An ce kudin na cikin sama da Bilyan 10 na kudin cinikin Fom daga wajen 'yan takara.
Mambobin kwamitin da suka mayar da kudaden sun hada da; 1. Mataimakin shugaban jam'iyyar na Kudu, Taofeeq Arapaja 2. Mataimakin shugaban jam'iyya na yankin Kudu maso yamma, Olasoji Adagundo, 3. Mataimakin jam'iyya na yankin Kudu maso kudu, Dan Orbih 4. Shugabar Matan jam'iyyar, Prof. Stella Affah-At 
Yayinda Adagunodo, Orbih da Effah-Attoe suka mayar N28.8 million da kowannesu ya samu, Arapaja ya mayar da N36m. A wasikar da suka aikewa shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, sun bayyana cewa basu san dalilin biyansu wadannan kudade ba.