2027: Atiku ya yi nuna sha'awar tsayawa takarar shugaban kasa a ADC
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi nuni da yiwuwar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027, ƙarƙashin haɗakar jam'iyyun adawa a jam'iyyar ADC.
Atiku, wanda ya fafata da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari a 2019, sannan ya ƙalubalanci Shugaba Bola Tinubu a 2023, ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin wani kwamiti ƙarƙashin jagorancin tsohon Minista Idris Abdullahi.
Ya sha alwashin cewa satar dukiyar ƙasa ko duk wani nau’i na cin hanci ba zai samu wurin zama ba a gwamnati da zai jagoranta.
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku ya ce: “Tura ta kai bango.”
Ya ƙara da cewa: “Za mu hukunta kowane mutum da ya ce zai sace dukiyar gwamnati ko ya aikata cin hanci da rashawa. Za mu yaƙe shi, wallahi. Tura ta kai bango ! Kowace ƙasa na cigaba amma Najeriya na fuskantar koma baya saboda wasu mutane kaɗan.”
“Wannan ne ya sa muka tabbatar cewa tsarin shugabancin rikon kwarya da muka kafa ya ƙunshi mutane masu gaskiya da amana. Daga nan ne za ku gane irin salon shugabancin da za mu yi.”
managarciya