Sojoji Sun Ceto Ƙarin  'Yan Matan Chibok  Biyu A Borno 

Sojoji Sun Ceto Ƙarin  'Yan Matan Chibok  Biyu A Borno 

Daga Sani Saleh Chinade, Maiduguri.

Rundunar sojin Najeriya a Borno ta sanar da kubutar da wasu 'yan matan Chibok biyu da 'yan ta'addar Boko Haram suka kwace da karfi daga dakin kwanansu na makarantar shekaru takwas da suka gabata.

Manjo-Janar Christopher Musa, kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadin Kai (OPHK) da ke arewa maso gabas ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Maiduguri.

Mista Musa, wanda ya kuma sanar da bude sabon sansanin karbar tubabbun ‘yan Boko Haram da ke mika wuya, ya ba da tabbacin cewa sabon sansanin na cikin wani wuri mai tsaro da sojoji za su iya tsare shi.

"Bisa kimantawa, mun duba wuraren da za a iya kare su yadda ya kamata," in ji Mista Musa.

Da yake karin haske kan ‘yan matan da aka ceto, babban kwamandan runduna ta 7 dake Maiduguri, Manjo-Janar Shuaibu Waidi, wanda ya gabatar da su ga manema labarai, ya ce za a mika su ga gwamnatin jihar Borno.

Manjo Janar Shuaibu ya ce, Yana Pogu mai lamba 19 a jerin ‘yan matan Chibok da aka sace, an ceto ta ne tun a ranar 29 ga watan Satumba tare da yara hudu;  ‘Yan mata biyu maza da tagwaye, a kauyen Mairari, a karamar hukumar Bama, da dakarun na 21 Armored Brigade suka yi, a yayin wani sintiri na share fage.

"Hakazalika, a ranar 2 ga Oktoba, aka kuma. Kara ceto Rejoice Sanki, wacce ke lamba 70 a jerin 'yan matan Chibok, sojojin bataliya 222 ne suka  ceto tare da 'ya'yanta guda biyu a yankin Kawuri," in ji Janar Waidi.

Ya ce' yanzu haka wadannan 'yan matan da aka ceto suna duba lafiyarsu tare da ‘ya’yansu domin a mika su ga gwamnatin Borno.

A halin yanzu za mu iya cewa, Sojojinu sun ceto ‘yan matan Chibok 13 a cikin watanni biyar da suka gabata.

Ya zuwa yanzu, daga cikin ‘yan matan na Chibok 276 da ‘yan ta’addan suka sace a shekarar 2014, kusan 96 ne ke hannun wadannan 'Yan ta'adda na Boko Haram.