Gwamnan Zamfara ya hana sarakuna bayar da izinin hakar ma'adinai a yankunansu
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya sanya hannu a dokar hanawa sarakuna ba da izinin hakar ma'adinai a fadin Zamfara gaba daya.
Gwamnan ya sanyawa dokar hannu a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jiha dake Gusau.
A bayanin da mai magana da yawun gwamnan jiha Sulaiman Bala Idris ya fitar ya bayyana cewa wannan dokar da gwamna ya sanyawa hannu za ta yaki wani silalen lamari da yake kara wutar 'yan bindiga a yankin.
A cewarsa umarnin ya dakatar da duk wata takardar izinin hakar ma'adinai "wadda ta hada da daidaikun mutane ko kamfani ko kungiyoyi dake aiyukkan hakar ma'adinai".
A jawabin gwamna a lokacin da yake sanyawa dokar hannu ya nuna an dauki matakin ne domin a samar da mafita ga abubuwan da amincewar ke haddasawa a jiha.
"A yau gwamnati ta amince ta yi maganin matsalar tsaro, kan haka na sanya dokar hanawa sarakuna a dukkan kananan hukumomin Zamfara 14 bayar da takardar izinin hakar ma'adinai.
"Babban Alkalin jiha ya ce harkar tonon ma'adinai yana cikin abubuwa na gaba-gaba dake bada gudunmuwa wurin kara tabarbarewar tsaro a jiha musamman a gefen 'yan bindigan daji," a cewar Dauda.
Ya ce gwamnatin da ta san abin da take yi dole ne ta dauki matakin hana hakar ma'adinai da ba bisa ka'ida ba wanda shi ne ya haifar da rikicin hakan ya sanya aka bayar da wannan umarnin.
managarciya