Home Uncategorized Bana samun nutsuwa a duk sanda nake nesa da al’ummar Sakkwato—-Sanata Wamakko

Bana samun nutsuwa a duk sanda nake nesa da al’ummar Sakkwato—-Sanata Wamakko

8
0
Bana samun nutsuwa a duk sanda nake nesa da al’ummar Sakkwato—-Sanata Wamakko

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya bayyana yanda jama’ar jihar Sakkwato suke cikin zuciyarsa kan haka baya son ya yi nisa da su domin mutuntawa da girmamawar da ke tsakaninsu.

Sanata Wamakko ya bayyana hakan  a yau jumu’a a gidansaDange Gawon Nama  a lokacin da ɗaruruwan masoya suka tarbo sa daga filin jirgin sama na tunawa da Sarkin musulmi Abubakar na uku a birnin jihar Sakkwato.
 
Tsohon Gwamnan Sakkwato ya shafe makwanni ukku  baya Sokoto sakamakon wata ziyarar aiki da yakai a ƙasar Ingila.

Ya ce “A lokacin da nake can  zuciyata tana nan Sakkwato tare da ku, saboda haka ne ma na  dawo domin haduwa da al’ummar Sakkwato masoyana.” a cewar Sanata cikin shauƙi da begen ganin magoya bayansa da ke ƙaunarsa kan alherinsa gare su.

An gudanar da addu’o’i na neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Sakkwato da kasa baki ɗaya daga bakin Mallam Bashir Gidan Kanawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here