Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta shawarci Aminu Ado da jami'an tsaro da su yi biyaiya ga hukuncin kotun Ɗaukaka Ƙara
Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da jami'an tsaro da sauran ɓangarori da su yi baiyaiya ga hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ta tabbatar da Sarki Muhammadu Sanusi ll a matsayin Sarkin Kano na 16.
A wani taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar ƴan jarida ta NUJ a Kano, Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Haruna Isa Dederi ya yi kira ga ɓangaren Bayero da su haɗa hannu da ɓangaren Sanusi don ci gaban Kano.
A cewar Dederi, hukuncin ya tabbatar da sahihancin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka na rusa masarautu biyar da kuma dawo da Sarki Sanusi.
Dederi ya jaddada cewa hukuncin ya rushe duk wasu hukunce-hukunce da umarni da babbar kotun tarayya ta yi a baya, inda ya kara da cewa hakan ya tabbatar da dokar da majalisar dokokin jihar Kano ta samar kan masarautu sahihiya ce.
"Haka nan, hukuncin ya halatta duk wasu matakai da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka bisa wannan doka," in ji Dederi.
"Wannan hukunci ya tabbatar da jajircewar mu wajen tabbatar da adalci, gaskiya, da bin doka. Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da ikon jihar Kano wajen nada sarakuna sannan ta rushe hukunce-hukunce da kotun taraiya ta yi saboda na hurumin ta ba ne," in ji shi.
managarciya