Kungiyar Arewa Za Ta Dakatar Da Kai Kayan Abinci Kudancin Najeriya

Kungiyar Arewa Za Ta Dakatar Da Kai Kayan Abinci Kudancin Najeriya

 
Kungiyar 'Northern Consensus Movement (NCM), mai rajin kare muradun 'yan Arewa, ta sha alwashin dakatar da kai kayan abinci daga Arewa zuwa Kudancin Najeriya. 
Kungiyar ta yi wannan barazanar ne biyo bayan wani wa'adi da dan rajin kare martabar yarbawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho ya ba al'ummar fulani da su fice daga kasar yarbawa cikin kwanaki goma ko ya dauki mataki.

Kungiyar ta ce za ta yi duk mai yiyuwa na dakatar da wannan kudirin na Igboho, amma idan wannan barazanar ta su ba ta ci ba, to za su dauki matakin fatattakar duk wasu yarbawa da ke zaune a garuruwan Arewa.
Shugaban kungiyar, Awwal Aliyu, ya yi wannan gargadin a ranar Alhamis a wani taron manema labarai. 

Bidiyon taron, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, ya mamaye kafofin watsa labarai da sada zumunta. 
A cikin bidiyon, anji Aliyu yana cewa: "Ba a jima da sako Sunday Igboho daga gidan gyaran hali ba, amma har ya fitar da sanarwar barazana ga al'ummar fulani da ke zaune a garuruwan yarbawa, tare da ba su umurnin fice wa daga yankins cikin kwanaki goma." 

"A wannan karon, kungiyar mu ta 'Northern Consensus Movement' za ta yi duk mai yiyuwa na ganin ta dakatar da hakan daga faruwa, amma idan ya ki ji, za mu dauki matakin fatattakar yarbawa daga garuruwan Arewa, in yaso, kowa ya zauna a kasar sa."