PDP ta karyata rahoton ƙasar Canada da ya ayyana ta da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci

PDP ta karyata rahoton ƙasar Canada da ya ayyana ta da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci

Jam’iyyar PDP ta karyata rahotannin da ke cewa wata kotu a Canada ta ayyana ta tare da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci, tana mai zargin hukuncin babu cikakken adalci  kuma ya shafi mutanen kirki a jam’iyyun.

Ɗan kwamitin koli na PDP, Timothy Osadolor, ya ce kotun ta wuce gona da iri wajen haɗa PDP da APC, yana mai kiran gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki lamarin da muhimmanci. Ya ce gazawar gwamnati wajen magance ta’addanci na sa Najeriya cikin haɗari.

Rahoton ya nuna cewa kotun tarayya ta Canada ta tabbatar da hukuncin kwamitin shige da ficenta, inda ta ki bai wa tsohon ɗan PDP da APC, Douglas Egharevba, mafaka saboda kasancewarsa memba na jam’iyyun tsawon shekaru goma. 

Kotun ta danganta PDP da APC da tashin hankali a siyasa, magudi, da kisan jama’a a lokacin zaɓe, musamman na shekarun 2003 da 2004.

Babu wata sanarwa daga APC da gwamnatin tarayya a hukumance, sai dai majiyar gwamnati ta ce ana jiran tabbatar da sahihancin hukuncin kafin fitar da martani.

 Masana sun yi gargadin cewa wannan hukunci na iya shafar martabar Najeriya a waje da kuma jefa matasa cikin matsala a harkokin tafiya da neman mafaka saboda alaƙarsu da jam’iyyun.