Tawagar Mataimakin Gwamnan Sakkwato ta yi hatsari mutum biyu sun rasu

Tawagar Mataimakin Gwamnan Sakkwato ta yi hatsari mutum biyu sun rasu

Tawagar Mataimakin Gwamnan Sakkwato Honarabul Idris Muhammad Gobir sun yi hatsari kan hanyar Sakkwato zuwa karamar hukumar Sabon Birni in da aka rasa mutum biyu a wannan Laraba.
Mutanen da suka rasa ransu a tafiyar akwai Mai daukar Hoto Buhari Usman da Dan sanda daya Mai suna Bargaja.
A bayanin da Managarciya ta samu motar kirar HILUX ta Kwacewa direba suka shiga daji ta birkice anan ne suka hadu da ajalinsu.
Sauran bayani zai zo daga baya.