'Yan bindiga dauke da manyan makamai saman babura fiye da 200 sun shiga kauyukkan karamar hukumar Sabon Birni guda biyar, in da suka kashe mutane 11 tare da garkuwa da mutum 7 a cikin kwana biyu.
Majiyar da ta shaidawa manema labarai halin da suke ciki ya ce "abin da zan sanar da kai muna cikin damuwa da tashin hankali a yankinmu 'yan bindiga sun matsa mana suna cin karensu ba babbaka gwamnatin Nijeriya ta tarayya da jiha sun kyale mu ana yi mana walakanci ba dauki ko kadan.
"A jiya(Lahadi) 'yan bindigar nan da yawansu sun tafi cikin garin Kurawa sun kashe mutum biyu, suka dawo Gumozo suka kashe uku, suka tafi Jijjira bayan bata kashi da su da mutanen gari suka kashe mutum daya.
"a Litinin kuma sun dawo saman babura sun fi 200 suka tafi kauyen Dan Garin Mutum suka kashe mutum biyar, a Gatawa mutum biyu bayan da aka yi dauki badadi tsakaninsu da mutanen gari da taimakon wasu sojoji aka kora mutanen wajen gari," a cewar majiyar.
Ya ce 'yan bindigar baka san adadin mutanen da suke tsare da su a wurinsu ba, sai dai ansamu nasarar an kubutar dacmutum bakwai da suka yi garkuwa da su a garin Dan Marke in da aka biya fansar dubu 100 ga duk mutum daya.
"muna cikin wahalar mutanen nan a ranar litinin data gabata sai da suka tare hanyar Sakkwato zuwa Sabon Birni sau 9, hakan ya sa ba wata motar da ta shigo nan ko ta fita, a kullum kuwa akalla sai an samu mota 20 da za su yi lodi zuwa Sakkwato, a yanzu kayan masarufi sun fara yanke mana, ka ajiye maganar abinci domin duk wanda yayi noman rani suna sanya shanunsu suna cinyewa tun daga Gangara abin ya kusa shigowa Sabon Birni," in ji shi.
Dan majalisar dokokin mai wakiltar Sabon Birni Honarabul Aminu Almustafa da aka sani da Boza ya tabbatar da hare-haren in da aka kashe mutane 11 ya ce 'yan bindigar sun matsa musu ba wani dauki daga gwamnati an kyale su ana kashinsu.
"a wata daya an kashe mana mutane sama da 20 ba wani mataki da muka ga an dauka game da magance mana matsalar da muke ciki muna ta magana an kyale mu da manema labarai muna fadin halin da muke ciki amma ba wani matakin a zo a gani," a cewarsa.
Duk kokarin jin tabakin jam'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Sakkwato DSP Sanusi Abubakar abin ya ci tura domin wayar shi ba ta zuwa.