Ministan Tsaron Nijeriya Ya Ƙaryata Hoton Da Aka Ce Shi Ne Ɗauke Da Bindiga
Ministan Tsaron Nijeriya Ya Ƙaryata Hoton Da Aka Ce Shi Ne Ɗauke Da Bindiga
Daga: Comrade Musa Garba Augie.
Wata sanarwa da mai taimaka wa ministan kan kafofin sada zumunta Mohammad Abdulkadri ya fitar ta ce masu son ta da zaune tsaye ne ke yada hoton da sunan Janar Magashi.
Ta kuma ce bincike ya gano cewa mutumin da ke cikin bidiyon shugaban kwalejin rundunar sojin Najeriya na kimiyya da fasaha da ke Makurɗi wato Nigerian Army College of Environmental Science and Technology (NACEST) Makurdi, wanda muƙaminsa ya ba shi damar riƙe makamai idan zai yi tafiya.
Sanarwar ta zayyano wasu abubuwa kamar kalar motar da mutumin ya shiga da takardar ke liƙe a jikin motar da ya dace a ce masu yaɗa bidiyon sun duba kafin su ayyana cewa ministan tsaron ne.
Ta ce ministan na amfani da motar jeep ce ƙirar Land Crusier kuma baƙa kamar sauran takwarorinsa ministoci.
Haka kuma, sanarwar ta ce ministan tsaron ba ya buƙatar ya ɗauki bindiga saboda kamar yadda aka gani a bidiyon saboda irin tsattsauran tsaron da ke tattare da muƙaminsa.
Ministan ya sanar da cewa al'ummar Najeriya su san cewa ana yin dukkan mai yiwuwa don ganin an daƙile ƴan bindiga da masu ta da ƙayar baya a ƙasar.
managarciya