Matsalar Man Fetur Ta Ƙara Sanya Mutane Cikin Wahala

Matsalar Man Fetur Ta Ƙara Sanya Mutane Cikin Wahala

Lamurra har yanzu ana ƙara shan wuya a Nijeriya bayan manyan jiragen da suka ɗauko man fetur guda 17 an ki raba man a ƙasa kamar yadda jaridar daily trust ta fahimta.
'Yan kasuwar man fetur sun kasa samun damar ba su man a rumbun kamfanin NNPC dake faɗin Nijeriya.
'Yan kasuwar da suka yanke shawarar sayen man a rumbun ajiye mai masu zaman kansu ana sayar musu sama da naira 165 a kowace lita.
A jihohin Lagos da Abuja 'yan black market suna sayarwa kowace lita kan 500 gidajen mai suna sayar da lita kan 250 kowace.
NNPC ta ɗaura alhakin wannan matsalar kan sufuri da lamurran man, manyan jiragen Gargo 17 da suka sauka a Lagos da Fatakwal an ƙi raba su har yanzu.
Mutane na cikin wahala kan ƙarancin man fetur da ake fama da shi a Nijeriya, litar mai ta kai 250 a Sakkwato kuma sai ka sha wahala ka samu.