Mun hallaka duk na jikin Bello Turji - CDS

Mun hallaka duk na jikin Bello Turji - CDS
Babban Hafsan Tsaron Ƙasa, CDS, Christopher Musa, ya bayyana cewa an hallaka dukka manyan kwamandoji a sansanin shugaban ƴan bindigan nan Bello Turji.
Musa ya bayyana hakan ne a wajen rufe taron da CDS ya shirya a Abuja a jiya Juma’a.
Ya ce wasu daga cikin kwamandojin ƴan ta’addan da aka kashe a samamen a ranar Alhamis din nan sun hada da Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu.
Ya kara da cewa nasarorin da sojoji su ka samu a Zamfara ya jefa Turji cikin wani yanayi na neman tsira.
“A wani samame da suka kai, sojojin sun kutsa cikin kauyukan Tufan da Mashima, inda su ka kara fatattakar kungiyoyin da ke dauke da makamai tare da kara tura su cikin dajin, in ji shi.