Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf Na Jihar Kano

Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kwamitin alkalan kotun ya tabbatar da hukuncin da kotun zaɓe ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Oluyemi Akintan Osadebay ta yanke wanda ya tsige Abba ranar 20 ga watan Satumba.
Bayan haka ne Kotun ta bayyana Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Kano da ƙuri'u mafi rinjaye, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.