Muddin Abubakar Malami zai tsaya takarar gwamnan jihar Kebbi, babu shakka za mu zabe shi - Al'ummar Jihar Kebbi

Muhammad, ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin wadanda suka bai wa shugaban kungiyar Malami Youth Forum, Alaramma Mustafa Shu'aibu shawarar neman takarar Majalissar Dokoki ta Jihar Kebbi, domin ya wakilci karamar hukumarsa ta Argungu. A karshe ya yi Kira kira ga Al'ummar Jihar, idan lokacin zabe ya yi, su fito su zabi Mai girma Ministan Shari'ar najeriya Abubakar Malami a matsayin sabon gwamna wanda zai kara farfado da martabar Jihar Kebbi.

Muddin Abubakar Malami zai tsaya takarar gwamnan jihar Kebbi, babu shakka za mu zabe shi - Al'ummar Jihar Kebbi
Abubakar Malami

Babban sakataren kungiyar "Malami Youth Forum" dake Jihar Kebbi a Najeriya, Muhammad Nuraddeen Shehu, ya ce muddin ministan shari'ar najeriya (SAN) Abubakar Malami zai nemi takarar gwamnan Jiharsu ta Kebbi, za su goya masa baya domin ya cancanta.

Nuraddeen Shehu, ya bayyana haka ne a yayin wata hira da wakilinmu Abdulrazak Ahmad Jibia ta wayar salula, inda ya kara da cewa "Tunda aka fara mulkin dimukradiyya, jihar kebbi bata taba samun wakilin da ya taimaki Al'umma irinsa ba."

"Abubakar Malami mutum ne wanda a koda yaushe ba shi da buri face kawo wa Al'umma ci gaban da zai taimake su. Wannan dalilin yasa muka kirkira  kungiya mai suna Malami Youth Forum domin mu kara wallafa kyawawan manufofinsa ta bangarori daban-daban domin mutanen Jihar Kebbi su kara fahimtar Mahimmancinsa da gudunmuwarsa a cikin Al'umma." Inji shi.

Muhammad, ya bayyana kansa a matsayin daya daga cikin wadanda suka bai wa shugaban kungiyar Malami Youth Forum, Alaramma Mustafa Shu'aibu shawarar neman takarar Majalissar Dokoki ta Jihar Kebbi, domin ya wakilci karamar hukumarsa ta Argungu.

A karshe ya yi Kira kira ga Al'ummar Jihar, idan lokacin zabe ya yi, su fito su zabi Mai girma Ministan Shari'ar najeriya Abubakar Malami a matsayin sabon gwamna wanda zai kara farfado da martabar Jihar Kebbi.