Dalilin Obasanjo Na Fadawa ‘Yan Najeriya Su Kauracewa Zaben Atiku Da Tambuwal

Dalilin Obasanjo Na Fadawa ‘Yan Najeriya Su Kauracewa Zaben Atiku Da Tambuwal

Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya nemi ‘yan Najeriya su raba kansu da zaben masu neman takarar da suke yi wa jama’a karya. 

Daily Trust ta rahotonta ta kawo  Olusegun Obasanjo yana mai kira ga al’umma su guji kada kuri’a ga duk wanda ke da'awar wasu suka saya masa fam din takara.
Tsohon shugaban ya fadi haka ne jihar Lagos a wurin ranar haihuwa na daya daga cikin manyan mutane a kabilar Yarbawa.

Rahoton ya ce  wanda ke takamar kyauta aka kawo masu fam sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar  da gwamnan Sokoto, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal da Peter Obi.
Akwai mai girma gwamnan Ribas, Nyesom Wike da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, kudin dukkansu bai yi ciwo kai ba wajen shiga takara. 
Wazirin Adamawa ya rike kujerar tsohon mataimakin shugaban kasa a gwamnatin PDP, daga baya ya samu sabani da mai gidansa kafin a shirya a 2019.