Kotu Ta Tura Ɗan Majalisa Alhassan Doguwa Gidan Yari

Kotu Ta Tura Ɗan Majalisa Alhassan Doguwa Gidan Yari

Wata Kotun Majistare da ke zamanta a Unguwar Nomansland ta Jihar Kano, ta tura Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhassan Ado Doguwa gidan wakafi.

Doguwa mai wakiltar kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada ya gurfana gaban kuliyar ce bisa zargin wasu laifuka masu alaka da hadin baki wajen aikata kisan kai, da raunata mutane da dama.

Haka kuma, ana zargin Doguwa da hannu a kunna wuta a ofishin jam’iyyar hamayya ta NNPP wadda ta yi sanadaiyyar kona wasu mutane da ke cikin ofishin.

A wata sanarwa da rundunar ’yan sandan jihar ta fitar ta ce Kwamishinan ’yan sandan jihar da ke lura da al’amuran zaben 2023 CP Muhammad Yakubu ne ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zarge-zargen.

Sanarwa ta ce ana zargin dan majalisar na da hannu a kisan wasu mutum uku tare da raunata wasu mutum takwas a Karamar Hukumar Doguwa ranar 26 ga watan Fabrairu a lokacin da ake karba tare da tattara sakamakon zaben dan majalisar.

An dai yi ta yada hotuna da bidiyon wasu mutane da ake zargi an harba da bindiga a shafukan sada zumunta.

Tun daga nan kuma rundunar ’yan sandan ta gayyaci dan majalisar domin gudanar da bincike kan batun.

Sanarwar ta ce bayan da dan majalisar ya ki amsa gayyatar ne, rundunar ’yan sandan jihar ta kama shi a filin jirgin saman Malam Aminu Kano da ke jihar.