Tinibu: Tambuwal Da Wasu 'Yan Majalisun Arewa 73 Basa Goyon Bayan Kudirin Haraji

Tinibu: Tambuwal Da Wasu 'Yan Majalisun Arewa 73 Basa Goyon Bayan Kudirin Haraji

 
Majalisar wakilan Najeriya ta sanar da dage tattaunawa kan kudirin gyaran haraji da aka shirya gudanarwa a ranar Talata, 3 ga Disamba. Matakin ya biyo bayan matsin lamba daga gwamnonin Arewacin Najeriya da wasu 'yan majalisar dokoki daga yankin. 
Rahoton Punch ya nuna cewa gwamnonin Arewa da wakilan yankin sun nuna rashin amincewarsu da kudirin, tare da bukatar neman karin shawarwari. 
Sanarwar dakatar da tattaunawar ta fito ne daga ofishin Sakataren Majalisar wakilai, Dr Yahaya Danzaria a ranar 30 ga Nuwamba. 
Takardar da sakataren majalisar ya fitar ta nuna cewa an dage zaman ne domin bai wa majalisar damar gudanar da karin shawarwari da masu ruwa da tsaki. 
“Mun yi hakane don tabbatar da an samu fahimtar juna daga kowane bangare,” - Hon. Yahaya Danzaria
'Yan majalisa 73 daga yankin Arewacin Najeriya sun nuna rashin goyon bayansu ga kudirin, ciki har da 'yan majalisa 48 daga Arewa maso Gabas da 24 daga Kano. 
The Cable ta wallafa cewa tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, ya goyi bayan dakatar da tattaunawar. 
Majalisar ta bayyana cewa sabon lokacin tattaunawar zai kasance nan gaba, inda za a bayar da sanarwa ga mambobin majalisar da sauran masu ruwa da tsaki.