Ku Zabi PDP A Zaben Da Ke Tafe Domin Tabbatar Da Zaman Lafiyar Sakkwato---Bello Goronyo
Jam'iyar PDP a jihar Sakkwato ta yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a jihar in da ta ce zaben wanda ke cike da rikici abin da yakai ga soke rumfunan zabe 300 sama da mutum dubu 400 ba su yi zabe ba, jihar ba ta taba ganin haka ba.
Shugaban jam'iyar na jiha Bello Aliyu Goronyo ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da ya yi a cibiyar 'yan jarida ta jiha ya ce abin mamaki ne yanda aka shigo da hatsaniya a siyasar jiha kuma hakan abin takaici ne da ba a saba da shi ba.
Ya yi kira ga magoya bayansu da su zama masu biyar doka su kuma kwantar da hankalinsu su fita su zabi PDP a zaben cike gurbi dana Gwamna dake tafe.
Ya ce kowa ya sani gwamnatin Sakkwato karkashin PDP ba goyon bayan hatsaniya za ta kuma cigaba da tabbatar da samun zaman lafiya a dukkan yankunan jihar Sakkwato.
Goronyo ya ce gwamnatinsu za ta ci gaba da mayar da hankali ga nauyin da yake saman kanta na kare rayuwa da dukiyoyin mutane har lokacin zabe a tabbatar ba a kawo rigima da cin zarafin mutane ba.
managarciya