Tambuwal Ya Gabatar Da Kasafin Naira Biliyan 188 Na Shekarar 2022
Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya gabatar da kasafin shekarar 2022 na naira biliyan 188 a gaban majalisar dokokin jiha.
Gwamnan ya ce aiyukkan yau da kullum za su laƙume sama da biliyan 75 kashi 40.3 na kasafin, ya yinda da manyan aiyukka za cinye biliyan 112 kashi 59.7 kenan.
Kasafin zai mayar da hankali ga ƙarasa aiyukkan da ake yi da kuma samar da sabbi.
Tambuwal ya warewa harkar ilmi kaso mafi yawa na biliyan 37 kaso 20 kenan sai lafiya biliyan 28 kaso 15 na ukun Aikin gona mai kaso 12 in da za a kashe biliyan 18.
Gwamna Tambuwal ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samu nasarori a ɓangarori da dama a kasafin kuɗi da ya gabata kan haka ya nemi a cigaba da ba shi goyon baya da haɗin kai.
Ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da mayar da hankali kan ilmi da tsaro da kaduwanci da noma da lafiya da sauran ɓangarorin cigaba a jihar ya kuma godewa 'yan majalisa kan goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa.