Gidauniyar El-Amin Ta Sha Alwashin Cigaba Da Tallafawa Marasa Lafiya Da Bada Tallafin Ilimi Ga 'Yayan Marasa Ƙarfi
Gidauniyar El-Amin Ta Sha Alwashin Cigaba Da Tallafawa Marasa Lafiya Da Bada Tallafin Ilimi Ga 'Yayan Marasa Ƙarfi
Daga Babangida Bisallah a Minna.
Shugaban gidauniyar El-Amin, Dakta Muhammad Babàngida ya bayyana cewar gidauniyarsa a shirye take wajen hadin guiwa da gidan radiyon Prestige dan tallafawa marasa lafiya.
Dakta Babangida ya bayyana hakan ne a lokacin da mai gabatar da shirin tallafi ga marasa lafiya, Malam Muhammad Ali ya jagoranci iyayen Oladele Aminat Anike da gidauniyar El-Amin ya ta dauki nauyin jinyar yi mata aikin zuciya a qasar Indiya.
Muhammad Ali, yace ba abinda zasu cewa gidauniyar sakamakon wannan namijin kokarin da suka yi na ceto rayuwar wannan karamar yarinyar, wanda sakamakon aikin da ya dauki shekaru uku kuma aka samu nasarar ceto ta, wanda tilas ne su godewa wannan gidauniya bisa jagorancin Dakta Muhammad Babangida jagoran makarantar El-Amin International da ke Minna.
Muhammad Ali ya cigaba da cewar bayan wannan akwai koke-koken marasa lafiya da dama, da hukumar gidan radiyon ta bada fili kyauta na musamman dan kai koken su ga jama'a, wanda da dama ana samun tallafin taro-sisi daga hannun jama'a da ake taimakawa marasa lafiya yanzu haka.
Dan haka idan da hali, za mu bukaci wannan gidauniyar da ta shigo dan xaukar nauyin masu manyan laluri dan taimaka musamman da yawan su ba karfi ke gare su ba, mu a bangaren mu muna bibiyan dukkan wadanda suka kawo kokensu ta hanyar kai wajen qwararrun likitoci dan yin gwaje-gwaje ga marasa lafiya, da kuma tabbatar an samar masu magungunan da suka dace.
A na shi jawabin, Dakta Muhammad Babangida yace mun kafa wannan gidauniyar ne dan tallafawa marasa qarfi wajen kula da marasa lafiya da xaukar nauyin karatun su. Yanzu haka muna da mutanen da mu ke daukar nauyin karatun su a jihar nan da dama, bayan waxanda wannan gidauniyar ta xauki nauyin jinyarsu akan lalurori daban-daban.
Kamar yadda mu ka dauki nauyin jinyar yarinyar nan na tsawon shekaru uku, haka kuma ina mai tabbatarwa iyayen yarinyar nan cewar mun dauke nauyin karatun ta, har zuwa inda Allah yaso.
Da yake karin haske ga manema labarai, kodineta mai kula da shirin gidauniyar a bangaren jin dadin jama'a, Malam Isah Bala Bwada yace a shekarar 2018 ne Dakta Muhammad Babangida ya ba mu umurnin nemo iyayen yarinyar nan a lokacin da yake sauraren shirin Prestige kan koken jama'a musamman marasa lafiya, bayan mun nemo su muka samu rahoton likitoci akan matsalar da zuciyarta ke fama da shi.
Mun kai su wani asibitin kwararru da ke Abuja, inda bayan gwaje-gwaje aka rubuta mana magunguna, muka saye, bayan 'yan watanni aka yi mata aikin farko, da yake yarinya ce karama bayan aikin farko aka sake rubuta mana magunguna kafin aiki na na biyu da ya shafi yoyon zuciyarta, wanda gidauniyar ta sake daukar wannan nauyinta zuwa kasar Indiya, mun samu nasara sosai a wannan aikin kuma Allah ya ba ta lafiya.
Bayan ita kuma akwai wata matashiya Margret Joseph da ita gidauniyar mu ta dauki nauyin yi mata aiki saboda ita ma ba ta da karfin kulawa da lalurar da ke damun ta. Wannan gidauniyar daga kafa zuwa yanzu mun dauki nauyin jinyar lalurorin mutane da dama, bayan daukar nauyin karatun 'yayan marasa karfi.
Mun zabi yin aiki da radio Prestige ne saboda suke gabatar da shirin koken jama'a masu dauke da lalurori, a kowani lokaci kofar mu a bude take kamar yadda jagoran shirin Dakta Muhammad Babangida ya tabbatar mana a yanzu.
Gidauniyar dai ko a farkon shekarar nan ta dauki dawainiyar aikin gyaran qafa ga wani xalibin mu wanda iyayen sa ba su karfi sosai a kasar Indiya wanda shi ma ya dawo har ya cigaba da karatunsa.
Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban gidauniyar El-Amin, Dakta Muhammad Babangida, yace gidauniyar su tafi mayar da hankali kan tallafin lafiya da na ilimi, domin su ne ginshikin cigaban kowani dan Adam, shi ilimi mataki ne na cigaban rayuwar dan Adam wanda idan babu lafiya duk wani kuduri ba za a samu damar cin masa ba, yanzu haka mun fi bayar da karfin mu a jihar Neja da Kaduna, inda ko a jihar Kaduna muna da jami'an da ke zagayawa asibitoci dan bada tallafi ga marasa lafiya, da wannan kudurin ne za mu cigaba da tafiyar da wannan gidauniyar.
managarciya