An Kara Harajin Shigo da Kayan Kasar Waje, Kayayyaki  Za Su Kara Tsada a Najeriya

An Kara Harajin Shigo da Kayan Kasar Waje, Kayayyaki  Za Su Kara Tsada a Najeriya

 

Babban bankin Najeriya (CBN) ya sake gyara fasalin farashin harajin shigo da kayayyaki zuwa Najeriya ta iyakokin ruwa da tudu. 

Harajin na kwastam kudade ne da ake karba daga hannun masu shigo da kayayyakin waje kafin sahale shigo da kayan da siyar dasu a Najeriya. 
Ana biyan kudaden ne ta bankunan kasuwanci ga Hukumar Kwastam ta Najeriya, wacce ke karba a madadin gwamnatin tarayya. 
Sabbin bayanai da aka buga a wata kafar kasuwancin gwamnatin tarayya  sun nuna cewa masu shigo da kaya daga Najeriya za su siya dala akan N1,457/$. Sabon farashin ya nuna karin kashi 2.99% daga yadda ya gabata a baya na N1,414.599 kan kowace dala a ranar Juma’a 10 ga Mayu, 2024. 
A karkashin sabon umarnin babban bankin kasar, hukumar kwastam za ta kididdige kudaden da za ta karba ne bisa la’akari da sauyin farashin musayar kudi da aka samu. 
Wannan gyara yana nufin masu shigo da kaya da suka cike ‘Form M’ a ranar Litinin, Mayu 13, 2024, za a caje su kan farashin da aka sabunta.
‘Form M’ tsari ne na tilas da ake cikawa ta yanar gizo don shigo da kaya na zahiri cikin kamar yadda hukumar kwastam ta tsara.