Shin Ya Dace Musulmai Su Nemi Ilmin Addinin Kirista Kamar Yadda Sarkin Musulmi Ya Ba Da Shawara?

Shin Ya Dace Musulmai Su Nemi Ilmin Addinin Kirista Kamar Yadda Sarkin Musulmi Ya Ba Da Shawara?
 

Sarkin Musulmi a shawarci Musulman da su dage da neman ilimin addinai daban-daban saboda kawo zaman lafiya 

Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya shawarci Musulmi da su nemi ilimin addinai da ba na su ba don samun zaman lafiya. 
Sultan ya kuma shawarci Musulmai da su nemi ilimin sanin Ubangiji don yin amfani da shi wurin zama mutane nagari, cewar Daily Trust.
Sarkin Musulman ya bayyana haka ne a yau Asabar 4 ga watan Nuwamba a Ilorin babban birnin jihar Kwara yayin lakcaR Usman Dan Fodio karo na 10. 
 
An kirkiri taron ne don martaba makon Usman Dan Fodio da aka fara a jihar Sokoto Wanda wannan shi ne karo na 10. 
Ya ce makasudin wannan lakca ta shekara an kirkire ta ne don kara wa Musulmai kwarin gwiwar neman ilimin addini da kuma amfani da shi. 
Ya ce: “An kafa masarautar Sokoto ce kan turbar neman ilimi ba rashinsa ba, saboda haka ya zama wajibi ga Musulmai su nemi ilimi kuma su yada zuwa ga ‘ya’yansu. “Hakan shi zai rage yawan jita-jita da karairayi idan har an nemi ilimin da ya dace na addini.” 
Sultan ya ce sun zabi Ilorin ne don nuna wa duniya cewa Musulunci abu daya ne kuma ba tare da bambanci ba, Royal News ta tattaro. 
Meyasa mu ka zabi Ilorin, wasu za su iya tambaya saboda akwai matsaloli na cewa mu kai shi Legas ne ko sauran birane. 
"Mun zo nan ne don ilmantar da ‘yan uwanmu don sanin irin sadaukarwa da kakanninmu su ka yi don dabbaka Musulunci.” 
Yayin gabatar da lakcan, Sheikh Zakir Naik ya yi jawabi kan sanin ubangiji a manyan addinan duniya.