Tinubu ne ya sa a ka jefi Buhari a Kano kuma mun yi alla-wadai - PDP

Tinubu ne ya sa a ka jefi Buhari a Kano kuma mun yi alla-wadai - PDP

Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi kakkausar suka kan harin da wasu bata-gari su ka kai wa ayarin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano, inda ya yi zargin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ne ya sa a ka yi wa shugaban haka.

A wata sanarwa da kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya fitar, ya ce harin da aka shirya ga shugaban kasa cin amanar kasa ne, kuma cin zarafi ne na kasa da kasa, wanda dole ne kowa ya yi Allah wadai da shi.

“Jam’iyyar mu ta firgita da cewa wannan harin na daga cikin yunkurin da mu ke zargin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC na yi wa fadar shugaban kasa zagon kasa, haifar da rudani, haddasa rikici a kasar nan, da kawo cikas ga gudanar da zaben 2023 da kuma dimokraɗiyyar mu; ganin cewa ba zai iya yin nasara ba a cikin lumana, yanci da adalci.

“PDP na kira ga ƴan Nijeriya da su lura da yadda Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi yunkurin dakile zuwan Shugaba Buhari  jihar Kano.

“Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ya nemi cin mutuncin shugaba Buhari da cutar da shi, a lokacin da ya ke gudanar da aikinsa a Kano.

“Ya kamata a lura cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC yana nuna kyama da kuma kalamai marasa daɗi ga shugaba Buhari tun bayan da ya furta cewa dole ne a yi zaɓen gaskiya da gaskiya a 2023.

“Bayan takaicin da Asiwaju Tinubu ke da shi na neman kwarin guiwa ko amincewa da tashin hankali ya taso ne saboda tunanin da ya ke da shi na cewa lokacinsa ne ya zama shugaban kasa, duk da rashin cancanta da gazawar da ya ke da ita.

"To, ahir ɗin Asiwaju kuma ya sani cewa babu wata barazana da zai yi wa ƴan Nijeriya wajen fafutukar su na ganin an kawo sauyi mai inganci a ƙasar nan," in ji sanarwar.