An ƙirƙiri wahalar fetur da sabunta kuɗi don kawo naƙasu ga zaɓen 2023----Tinubu

An ƙirƙiri wahalar fetur da sabunta kuɗi don kawo naƙasu ga zaɓen 2023----Tinubu

 

Dan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matsalar karancin man fetur da kuma sauya fasalin takardar kudin Naira a matsayin wani shiri na yi wa zaben 2023 zagon-kasa.

 
Tinubu na magana ne a yayin yakin neman zabensa a birnin Abeokuta na jihar Ogun a jiya Laraba.
 
A cewarsa, "wasu ba sa san a gudanar da wannan zaben, suna son yi wa zaben zagon-kasa. 
 
"Shin za ku bari hakan ya faru?,"  Tinubu ya tambayi dandazon magoya bayansa da suka hallara a filin wasa na MKO Abiola da ke Abeokuta.
 
Tsohon gwamnan na jihar Lagos ɗin ya lashi takobin cewa, duk da wahalar man fetur, ƴan Najeriya za su yi tattaki har zuwa rumfunan zaɓe don su kada kuri’u.
 
Tinubun ya bayyana kwarin guiwar samun nasara a zaben mai zuwa "duk kuwa da kirkirar karancin man fetur din da sauya fasalin takardar kudin Naira."