Ƙungiyar NRC Da IFRC Sun Horas Da Matasa 30 A Sakkwato

A lokacin horaswar jami'in da ke kula da Lahiya na kungiyar  Dakta Salisu Buhari na Jami'ar Usmanu Dan fodio ya gabatar da kasidu da hotuna  domin samun fahimtar aikin da za su je su yi.   Anasa jawabin sakataren kungiyar dake nan jihar sakkwato Malam Shehu Dake ya ja hankalinsu da su jajirce su yi abun da aka koyar da su. 

Ƙungiyar NRC Da IFRC Sun Horas Da Matasa 30 A Sakkwato
Ƙungiyar NRC Da IFRC Sun Horas Da Matasa 30 A Sakkwato
Daga M. A Faruk Sokoto

Kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Duniya NRC da IFRC  sun horas da matasa 30 a yankunan ƙananan hukumomin Yabo, Shagari da Bodinga domin su shiga lungu da sako su fadakar da jama'a hanyoyin kariya da ɗaukar matakin kan  annobar gudanawa da amai watau (cholera) a yankunansu.  

A lokacin horaswar jami'in da ke kula da Lahiya na kungiyar  Dakta Salisu Buhari na Jami'ar Usmanu Dan fodio ya gabatar da kasidu da hotuna  domin samun fahimtar aikin da za su je su yi.  
Anasa jawabin sakataren kungiyar dake nan jihar sakkwato Malam Shehu Dake ya ja hankalinsu da su jajirce su yi abun da aka koyar da su. 
A jawaban su daban-daban sarakunan Yabo da shagari da Bodinga sun yaba dakuma ba da tabbacin hadin kan jama'ar yankunasu wajen gudanar da wannan fadakarwa wadda za ta  ɗauki Watanni 4 ana gudanarwa.