'Yan Sanda A Kano Sun Cafke Masu Safarar Fetur Ga 'Yan Bindigar Katsina
'Yan Sanda A Kano Sun Cafke Masu Safarar Fetur Ga 'Yan Bindigar Katsina
Daga muhammad Ibrahim, Kano
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta ce ta cafke wasu mutane da take zargin suna kai wa ƴan bindigar Katsina man fetur.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Talatar da ta gabata,
Ta cikin sanarwar Kiyawa ya ce ƴan sanda sun kama mutanen ne su biyu Musbahu Rabi’u mai shekaru 31 da kuma Jamilu Abdullahi mai shekaru 37.
Haka kuma sanarwar ta ce, mutanen mazauna ƙaramar hukumar Jibiya ne ta jihar Katsina, inda aka cafke su lokacin da suke sanya jarakunan fetur a buhuna tare zuba su a mota ƙirar J5.
Kazalika sanarwar ta ce, mutanen sun ce suna sayen man ne a Kano tare da kai shi Katsina kasancewar an hana sayar da shi a jarakuna a can shi ya sanya suke ɓoye shi a buhun sukari.
managarciya